Matashiya Da Aurenta Ya Mutu Bayan Watanni 7 Ta Caccaki Tsohon Mijinta a Facebook

Matashiya Da Aurenta Ya Mutu Bayan Watanni 7 Ta Caccaki Tsohon Mijinta a Facebook

  • Wata yar Najeriya mai suna Hazel Ajuamiwe, ta caccaki tsohon mijinta wanda ta yi ikirarin cewa yana kunyar nunata ga duniya
  • Matar wacce aurenta ya mutu bayan watanni bakwai ta ce ji take kamar tsawon shekaru bakwai ta yi ana musguna mata
  • Dogon rubutun da Hazel ta yi a Facebook ya haddasa cece-kuce inda mutane da dama suka mara mata baya

Wata matashiya yar Najeriya wacce aurenta ya mutu bayan watanni bakwai ta yi wa tsohon mijinta wankin babban bargo a Facebook kan zunuban da ya aikata a rayuwar aurensu.

Bazawarar, Hazel Ajuamiwe, wacce ta fito daga yankin Umuahia, ta wallafa hotunan aurensu wanda ta ce tsohon mijinta baya so duniya ta gani.

Matashiya da tsohon mijinta
Matashiya Da Aurenta Ya Mutu Bayan Watanni 7 Ta Caccaki Tsohon Mijinta a Facebook Hoto: Hazel Ajuamiwe
Asali: Facebook

Hazel, wacce ta yi ikirarin cewa shugaban kungiyar yan aware na IPOB, Nnamdi Kanu dan uwanta ne, ta ce tsohon mijinta na kunyar kasancewarsu tare sannan ta jero misalai da yawa a zaman aurensu.

Kara karanta wannan

Yar Shekaru 13 Ta Kashe Miliyan N40 Da Iyayenta Suka Tara Wajen Buga Wasanni

A wani dogon rubutu da ta wallafa a Facebook, ta ce watanni bakwai da suka yi a aurensu ya yi kama da shekaru na zalunci. Ta kara da cewar tsohon mijin nata na yawan kwatanta ta da tsoffin yan matansa kuma bai taba yaba ma kamanninta ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani bangare na rubutunta na cewa:

"A karo na gaba wani da ban sani ba ya fada mani cewa ina da kyau; na kadu da jin haka. Na manta cewa ina da kyau saboda mutum daya da ya kamata ace yana yaba mani yana yawan kushe ni da muzantani.
"Ya kasance abun farin ciki bayan ganin na samu kaina...kuma yanzu muryata ta kara karfi fiye da baya.
"Auren watanni 7 da ya yi kama da shekaru 7 na azaba..."

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

Matashi Mai Samun N100k Ya Bukaci Budurwa Mai Samun N34m Ta Aje Aikinta Ta Aure Shi

Mbemsi Emmanuel ya ce:

"Wato na matsu na ji, ta yaya kuka hadu? Shin akwai alamun danja kafin ku yi aure? Ina ganin wannan zai taimaka mana mu da bamu yi aure ba don sanin abun da za mu duba kafin mu amsa da eh."

Fatty Newton ta ce:

"Ki yi magana! Ki bari a ji muryarki! Da dama za su iya amfana daga karfin gwiwarki don su tashi daga kan teburin da baya masu amfani kuma. Na yaba maki."

Eric Uchenna Chimara ta ce:

"Lallai kina da jarumta. Barin auren da wuri ya nuna kina da karfin zuciya."

Yar shekaru 13 ta yashe iyayenta, ta buga wasanni da miliyan N40 da suka tara

A wani labari na daban, wata yarinya yar shekaru 13 daga China ta yi wa iyayenta bazata sakamakon dabi'antuwa da ta yi da buga wasanni ta intanet.

Matashiyar dai ta faki ido sannan ta dauke katin bankin mahaifiyarta inda ta dunga biyan kudin buga wasanni har ta kai ga cin miliyan N40 cikin watanni hudu kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng