Shugaba Tinubu Ya Gana da Sarakunan Gargajiya a Najeriya, Sultan Ya Magantu
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Sarakunan gargajiya a Najeriya a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
- Ana tsammanin Tinubu zai taɓo batun haɗa kan kasa da kuma tsamo Najeriya daga yanayin da take ciki a zamansa da Sarakunan
- Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma jagoran tafiyar ya tabbatar wa shugaban kasa cewa suna tare da shi
FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana yanzu haka da manyan Sarakuna da wakilansu daga dukkan sassan Najeriya a Aso Rock da ke Abuja.
Punch ta rahoto cewa wannan taro da ya gudana ranar Jumu'a, 9 ga watan Yuni, 2023, wani bangare ne na zaman tattaunawa da Tinubu ke jagoranta da masu ruwa da tsaki a ƙasar nan.
A wurin wannan taro, ana tsammanin Tinubu zai taɓo batun da ya shafi tsamo ƙasar nan daga cikin ƙunci da haɗin kai, kamar ya jaddada a jawabinsa na ranar bikin rantsuwa.
Sarkin Musulmi ya yi jawabin kan abinda ya sa suka je wurin Tinubu
A jawabin buɗe taro, mai alfarma Sarkin Musulmai (Sultan na Sakkwato), Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya ce sun ziyarci shugaba Tinubu domin taya shi murnar fara aiki a matsayin shugaban ƙasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sarkin Musulmin, wanda ya jagoranci takwarorinsa zuwa wurin shugaban kasa, ya kuma tabbatarwa Tinubu cewa suna tare da shi 100% a kudurinsa na sake gina ƙasa.
Sultan ya ƙara da cewa zasu zauna cikin shiri a ko wane lokaci domin amsa kiran shugaban ƙasa a duk lokacin da yake buƙatar taimakonsu.
Basaraken ya nuna cewa Sarakuna na da ƙwarin guiwar Tinubu na da gogewar aiki da zai iya karkato da akalar Najeriya ta dawo kan turbar ci gaba, inda ya ce zasu mara masa baya wajen cika alkawarin da ya ɗauka.
Babban Sarkin Yarbawa ya roki Tinubu
A nasa jawabin babban basakaren yarbawa, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Adewusi, ya roki shugaban ƙasa ya jawo Sarakuna a jiki wajen magance matsalar tsaro.
Mataimakin shugaban ƙasa, Ƙashim Shettima, Sakataren gwamnatin tarayya, Geoge Akume, da babban Sakataren fadar shugaban ƙasa, Tijjani Umar sun halarci taron.
Sarakunan da suka halarci taron
Sarakunan da aka hanga sun gana da Tinubu sun haɗa da Sarkin Kano, Obi na Masarautar Onitcha, Sarkin Tiv, Etdu na Nupe, Deji na Akure, Shehun Borno, Sarkin Zazzau da sauransu.
Gwamnan Jihar Filato Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata Daga Bakin Aiki
A wani labarin kuma Sabon gwamnan Filato ya dakatar da sabbin ma'aikatan da aka ɗauka aiki tun a 2022.
Gwamna Caleb Mutfwang ya soke naɗe-naɗen manyan Sakatarori da tsohuwar gwamnati ta yi. A wata sanarwa, ya bayyana dalilan da ya dogara da su har ya ɗauki wannan matakai.
Asali: Legit.ng