Rusau: Dubu ta Cika, 'Yan Sanda Sun Sake Kwamushe Mutane 57 Bisa Zargin Dibar Ganima

Rusau: Dubu ta Cika, 'Yan Sanda Sun Sake Kwamushe Mutane 57 Bisa Zargin Dibar Ganima

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sake kama wasu da ake zargi da satar kayan mutane yayin rushe shaguna da ake yi a Kano
  • Rundunar ta tabbatar da kama karin mutane 57 da suke da alaka da sace-sacen dukiyoyin al'umma a yayin rusau
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya bukaci hadin kan al'umma don kawo karshen sace-sacen

Jihar Kano - Rundunar'yan sandan jihar Kano a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyi ta sake kama wasu matasa da ake zargi da satar dukiyar mutane a lokacin rushe-rushe da gwamnatin jihar ke yi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ta kama karin mutane 57 da ake zargi da wuce gona da iri da kuma satar dukiyar mutane.

'Yan sanda sun kama matasa 57 da ake zargi da satar dukiyoyi a Kano
Rundunar ’Yan Sanda Ta Kama Mutane Da Dama Bisa Zargin Sata. Hoto: Channels TV.
Asali: Twitter

Wannan samamen na zuwa ne bayan samun bayanai cewa matasa suna amfani da damar rushe wasu gine-gine da gwamnatin jihar ke yi don sata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano Za Ta Cigaba da Rushe-Rushe Bayan Rade-Radin Tilasta Dakatarwa

Kamen da aka yi ya tabbatar da yawan mutanen da aka kama har 106 wadanda dukkansu an gurfanar da su a gaban kotun Magistare da ke Kano, cewar gidan talabijin ta Channels.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kama matasan da muggan makamai da suke amfani da su wurin satar

An samu muggan makamai da sauran abubuwan da wadanda ake zargin suka yi amfani da su yayin aiwatar da laifukan.

Rundunar ta kuma shawarci wadanda abin ya shafa da su garzaya Ofishin Binciken Laifuka (CID) da ke Bompai a Kano don yin bayani da kuma nuna kayan nasu.

Rundunar ta ce hakan zai taimaka wurin yin bincike da kuma samun sauran kayan da aka sace.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya nemi hadin kan iyaye don dakile sace-sace

A wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Kwamishinan 'yan sandan jihar ya godewa mutane da hadin kai da suke ba wa jami'an tsaro inda ya tabbatar da cewa za su ci gaba da tsaron al'umma da dukiyoyinsu.

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya kuma godewa wadanda suka taimaka wajen samun bayanai, inda ya bayyana muhimmancin hada kai da jami'an tsaro wurin tabbatar da zaman lafiya a cikin al'umma.

Ya roki iyaye da su gargadi yaransu da kuma ci gaba da kula da harkokinsu don ganin an dakile irin wadannan sace-sace a cikin al'umma.

Kananan ’Yan Kasuwa Sun More, Abba Gida-Gida Ya Yafe Musu Biyan Haraji

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce masu kananan sana'o'i ba za su biya kudin haraji ba.

Gwamnan ya bayyana cewa duk wanda baya samun N30,000 zuwa sama an dauke masa biyan haraji da za a fara a watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.