Ko Gezau: Maryam Abacha Ta Ce Ba Ta Kewar Fadar Shugaban Kasa, Ta Koka Yadda Mutane Ke Muzanta Mijinta
- Bayan shekaru 25 da rasuwar tsohon shugaban kasa, Sani Abacha, mai dakinsa ta bayyana yadda ta kasance
- Maryam Abacha ta ce ba ta taba kewar fadar shugaban kasar ba yayin da ta ce dama sun saba yawo a fadin kasar
- Ta bayyana yadda ake fadan abubuwa marasa kyau akan mijinta da cewa wannan ba komai ba ne haka mutane suke
FCT, Abuja - Maryam Abacha, matar marigayi tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Sani Abacha ta ce tun bayan mutuwar mijin nata, ba ta taba kewar fadar shugaban kasa ba ko sau daya.
Maryam ta bayyana haka ne a ranar Alhamis 8 ga watan Yuni yayin hirarta da BBC Hausa kan abubuwan da ta ke tunawa a matsayin matar tsohon shugaban kasa.
Ta ce zamanta a fadar shugaban kasa wannan ta saba da shi kuma ya zama kamar rayuwarta ne inda ta ce mahaifinta ma ma'aikacin gwamanti ne sun yi yawo sosai a kasar, cewar Daily Trust.
Ta ce ba ta taba kewar fadar shugaban kasa ba tun lokacin mutuwar mjinta
A cewarta:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ba na kewar komai a fadar shugaban kasa, kin san a matsayina na matar soja munyi yawo wurare daban-daban.
"Mahaifina ma'aikacin gwamnati ne, kafin ma na auri marigayin mun saba yawo wurare daban-daban na kasar nan.
"Tabbas akwai daukaka a fadar shugaban kasa amma kuma akwai matsaloli musamman na siyasa, ai shi soja ba dan siyasa ba ne amma idan ka shiga wannan gida ai ta siyasa ce, amma babu abin da na ke kewa.
Da aka tambaye ta ko me take yi yanzu, Maryam Abacha ta ce tana rubuce-rubuce a ofishinta kuma har da mai taimaka mata ta na da shi saboda ita ba ta saba da zama haka ba.
Na saba da bakaken maganganu kan marigayin miji na
"Abin Da Ciwo": Wata Da Ke Saudiyya Ta Yi Kuka Ganin Halin Da Yayanta Ke Ciki Duk Da Tana Turo Kudi Duk Wata
Ta ce ta saba da munanan abubuwa da 'yan Najeriya suke fada akan marigayin, ta ce hakan ba komai ba ne a wurin 'yan siyasa, mutane suna fadan abubuwa masu kyau da marasa kyau.
Marigayi Sani Abacha ya cika shekaru 25 da rasuwa a jiya Alhamis 8 ga watan Yuni, ya rasu a ranar 8 ga watan Yuni na shekarar 1998 a fadar shugaban kasa da ke babban birnin Tarayya Abuja.
Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Karar Mohammad Sani Abacha
A wani labarin, kotun koli ta yanke hukunci na karshe akan karar Mohammed Sani Abacha da aka yi.
Gwamnatin Tarayya ta shigar da kara don kwato makudan kudade da ake zargi marigayi Sani Abacha ya yi sama da su.
Asali: Legit.ng