Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Sanatan Najeriya Mai Karfin Fada A Ji Ya Rasu A Asibitin Amurka
- Najeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun 'yan majalisarta, Sanata Annie Okonkwo, wanda ya rasu a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni
- Fitaccen Sanatan, wanda ya rasu yana da shekaru 63, ya wakilci yankin Anambra Ta Tsakiya a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011
- An bayyana cewa ya rasu ne a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a ƙasar Amurka, bayan ya sha fama da rashin lafiya
Tsohon Sanata mai wakiltar Anambra ta tsakiya a Majalisar Dattawa, Sanata Annie Okonkwo ya rasu a kasar Amurka.
An ba da rahoton rasuwar tasa ne a kasar Amurka bayan fama da rashin lafiya mai tsanani da ya yi.
Wani ɗan uwansa da ya nemi a sakaya sunansa ne ya shaidawa jaridar Vanguard ta wayar tarho tabbacin rasuwar ta Sanata Okonkwo.
Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu
Marigayin dai a kwanakin baya, wato a ranar 23 ga Mayu, 2023, ya yi bikin cikarsa shekaru 63 a duniya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani saƙo da wani daga cikin danginsa, ya aikewa Daily SUN na cewa:
“Dukkannin iyalan Okonkwo na ƙauyen Iruebenebe na Ojoto, na sanar da rasuwar Cif Annie Okonkwo. Lallai Ojoto ta rasa babban ginshiƙin siyasa.”
Wanene Sanata Okonkwo?
Marigayin ɗan majalisar, ɗan asalin Ojoto ne a Ƙaramar Hukumar Idemili ta Kudu, kuma ya kasance a majalisar dattawa tsakanin 2007 zuwa 2011 a karkashin tutar jam’iyyar PDP.
Baya ga harkokin siyasa, Sanata Okonkwo ya samu nasara a fannin masana’antu a matsayinsa na ɗan kasuwa da ya yi fice wajen saka hannun jari a harkar sadarwa, cinikin kayayyaki, gidaje, mai da iskar gas.
Shi ne mamallakin kamfanoni da dama irinsu Reliance Telecoms, Clemco Industries, Sunflower Nigeria da kamfanin mai na Pentagon Oil da sauransu.
Karatun Sanata Okonkwo
Sanata Okonkwo ya samu difloma mai zurfi a fannin kasuwanci da difloma mai zurfi a fannin shari'ar kasuwanci, daga Jami'ar Legas).
Haka nan kuma tsohon dalibi ne a babbar Makarantar Kasuwanci ta Harvard, inda kuma ya samu Difloma mai zurfi a fannin Gudanarwa.
Babban Limamin Juma'a ya rasu Kano
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji cewa an rasa babban Limamin Juma'a na masallacin Fagge da ke cikin birnin Kano.
Sheikh Nasir Muhammad Nasir, wanda kuma tsohon Wazirin Kano ne, ya rasu yana da shekaru 87 a duniya bayan fama da rashin lafiya.
Asali: Legit.ng