Tinubu Ya Umarci Shettima Ya Fito da Tsarin Taimakon Talaka Bayan Janye Tallafin Fetur

Tinubu Ya Umarci Shettima Ya Fito da Tsarin Taimakon Talaka Bayan Janye Tallafin Fetur

  • Bola Ahmed Tinubu ya ba NEC umarnin su kawo dabarun da gwamnatin tarayya za ta taimaki talaka
  • A doka, Kashim Shettima ya ke jagorantar majalisar a matsayinsa na mataimakin shugaban Najeriya
  • Gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur wanda hakan ya sake jefa al’umma a mawuyacin hali

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci majalisar NEC a karkashin Kashim Shettima, ta fito da yadda za a rage radadin cire tallafin fetur.

Tashar talabijin Channels ta ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai jagoranci yadda za a bullo da tsarin da za su jika makoshin talaka.

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya shaida haka a ranar Laraba bayan shugaban Najeriya ya zauna da manyan ‘yan kasuwan mai a fadar Aso Rock.

Tinubu
Bola Tinubu tare da Gwamnoni Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Abiodun wanda ya taba zama shugaban kungiyar ‘yan kasuwan na mai ya ce ‘yan kasuwa sun nuna goyon cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi.

Kara karanta wannan

An Samu Labarin Abin da Bola Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni a Game da Talakawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan kasuwa za su raba motoci

Har ila yau, rahoton ya ce ‘yan kasuwan sun yi alkawarin bada gudumuwar manyan motocin daukar mutane 50 zuwa 100 domin a taimakai talaka.

Kowace mota ta kai kusan Naira miliyan 100, saboda haka za a kashe kimanin N10bn a sayen motocin masu daukar akalla mutane 50 a lokaci guda.

Da gwamnatin tarayya ta yi zama da TUC, ‘yan kasuwan sun gabatar da bukatarsu cewa a kara albashi ta yadda babu wanda zai karbi kasa da N200, 000.

Punch ta ce a dalilin haka ne Shugaba Tinubu ya ba majalisar NEC umarnin ta kawo dabarun da za fito da su domin a iya ragewa talaka wahalar rayuwa.

Baya ga haka, majalisar da ke kula da tattalin arzikin zai yi nazarin karin mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan 'Yan Kasuwar Man Fetur Kan Batun Cire Tallafi

Shugaban kungiyar NGF kuma Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya shaida cewa Shettima aka ba aikin kawowa talaka saukin rayuwa.

Wannan majalisa na kunshe da mataimakin shugaban kasa a matsayin shugabanta, sai Gwamnonin jihohi 36, gwamnan CBN da wasu jami’an gwamnati.

Talauci, rashin gaskiya ko ganganci?

A jihar Kano, an ji labari mutane musamman ‘yan zaman banza su na bi inda aka ruguza gine-gine domin su sace kaya, a ciki an samu wanda ya mutu.

Marigayin da wasu yara sun fito da fallen kwano, rodi da kofofi, amma sai aka yi rashin sa’a, kwanansa sun kare, sai wata tirela ta murkushe shi a nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng