Bidiyon Wasu Masoya Suna Shakatawa a Ɗakin Otel Ya Girgiza Intanet

Bidiyon Wasu Masoya Suna Shakatawa a Ɗakin Otel Ya Girgiza Intanet

  • Bidiyon wata zankaɗediyar budurwa 'yar Najeriya tare da ɗan matashin saurayinta a ɗakin Otal ya girgiza mutane a soshiyal midiya
  • Budurwar wacce ta wallafa bidiyon kowa ya gani, ta ɗauki kanta da wani ɗan matashi wanda babu tantama saurayinta ne yayin da ya yi nisa a bacci
  • Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun nuna mamakin ƙarancin shekarun ɗan matashin saurayin, inda suka riƙa wasan barkwanci da shi

Wata matashiyar 'yar Najeriya kuma kyakkyawar budurwa ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya kan wani bidiyo da ta ɗauki kanta da wani ɗan saurayi da take kira da, "Papi na."

A wani shafin dandalin TikTok @thatgirlese18, budurwan ta wallafa bidiyon wanda ya nuna ita da masoyinta sun kwanta kan gado a wani wuri da ake kyautata zaton ɗakin Otal ne.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Aiki

Dakin Otel.
Bidiyon Wasu Masoya Suna Shakatawa a Ɗakin Otel Ya Girgiza Intanet Hoto: @thatgirlese18
Asali: TikTok

Yayin da ɗan bawan Allah ya yi nisa a bacci harda wangame baki, ita budurwan kam idonta biyu kuma ta yi amfani da wannan damar wajen ɗaukar bidiyonsu tare.

Ta waiga ta kalle shi ta gani ko ya farka daga bacci amma ta ga mutumi na ta sharar barci abinsa, daga nan ta ci gaba da ɗaukar bidiyonta tana ƙara gyarawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bidiyon ya ja hankalin masu amfani da kafar TikTok kuma mutane da yawa sun tofa albarkacin bakinsu musamman ganin matashin bai da wasu shekaru da yawa.

Kalli bidiyon masoyan a nan

Martanin wasu mutane kan bidiyon budurwar da matashin saurayin

Fawaz ya ce:

"Ya haka ne kar ki rufe masa baki, ki bar ɗan bawan Allah ya huta mana."

Ola Para ta ce:

"Haba dai wannan ba saurayinki bane, ai ƙaramin yaro ne, inda ya cika matashi kuma saurayi ba zai yi kalar wannam barcin ba."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Je da Kansa, Ya Baiwa Waɗanda Harin Yan Bindiga Ya Shafa Tallafin Kuɗi da Abinci

Glory Bilz ta rubuta cewa:

"Zamani ya kawo mu mata basu barin mutun ya cika shekara 18 kafin su fara kiransa da Papi na."

Vawulence ya maida martani da cewa:

"A duk abinda zaka yi a rayuwa kar ka kuskura mace ta riƙa rigaka farkawa daga bacci."

"Ba Wayau": Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa

A wani labarin kuma Wata zankadediyar budurwa ta bar Saurayin da ya nuna mata kauna da cizon yatsa bayan ta buga masa damfarar da ta sha kansa.

A cikin wata hira da aka fitar, budurwar mai suna Chiwendu ta tura masa lambar asusun ajiya a banki domin ya turo mata kuɗin mota.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel