Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Yan Kasuwar Man Fetur Kan Cire Tallafi

Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Yan Kasuwar Man Fetur Kan Cire Tallafi

  • Shugaban ƙasa Tinubu ya sa labule da 'yan kasuwar man Fetur a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja ranar Laraba, 7 ga watan Yuni, 2023
  • Gwamnan Ogun, wanda ke shugabantar ƙungiyar 'yan kasuwan man ne ya jagorance su zuwa fadar shugaban kasa
  • Ana ganin wannan ganawa zata maida hankali kan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi da kuma abinda ya biyo baya

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da manyan 'yan kasuwar man fetur a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

A rahoton Channels tv, Gwamna jihar Ogun kuma shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar mai, Dapo Abiodun, ne ya jagoranci 'yan kasuwar zuwa wurin ganawa shugaban ƙasa.

Shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Manyan Yan Kasuwar Man Fetur Kan Cire Tallafi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wannan ganawa ta shugaba Tinubu da yan kasuwan na zuwa ne yayin da ake cece-kuce da yunkurin nuna adawa ta hanya daban-daban da cire tallafin man fetur (PMS) a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Gwamnonin Jihohi 36 a Karon Farko, Bayanai Sun Fito

Tun a jawabinsa na ranar bikin rantsarwa, 29 ga watan Mayu, a Eagle Square, shugaban ƙasa, Tinubu, ya ƙara tabbatar da cewa FG ta tsame hannunta daga biyan tallafin mai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ba ta ware kuɗin tallafin mai ba a kasafin 2023.

Ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta ware tallafin ne iyakar watan Yuni, ba wanda ya wuce haka, sai dai da yawan yan Najeriya sun ɗauka sai 1 ga watan Yuli, farashin litar mai zai ɗaga.

Amma nan take bayan kalaman shugaban kasa a wurin rantsarwa, aka fara cunkoson layin sayen man Fetur yayin da 'yan kasuwa suka fara ɓoyewa suna ƙara farashin kowace lita.

Tuni dai gidajen man 'yan kasuwa suka koma siyar da lita a kan farashi sama da N500 bayan kamfanin mai na kasa NNPCL ya ƙara farashi da kuma kalaman shugaba Tinubu, rahoton Vanguard ya tattaro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya

An Rantsar Da Gorge Akume a Matsayin Sabon SGF, Ya Daukarwa Yan Najeriya Manyan Alkawara

A wani rahoton na daban Shugaba Tinubu ya rantsar da sabon Sakataren gwamnatin tarayyada ya naɗa, George Akume.

Bayan karban rantsuwar kama aiki, Akume ya yi alkawari cewa ba zai ba yan Najeriya, Shugaban kasa Tinubu da jam'iyyarsa ta All Progressive Congress (APC) kunya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262