Cire Tallafi: Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba

Cire Tallafi: Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cire tallafi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu a yayin bikin rantsar da shi
  • Dillalan man fetur a kasar sun rufe gidajen mansu yayin da wasu suka kara farashin litar mai a gidajen mai da dama
  • NLC ta yi wani ganawa ta gaggawa da Gwamnatin Tarayya amma ba a cimma matsaya ba a yayin ganawar

Sanarwar da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi akan cire tallafin mai ya jawo ‘yan kasuwa sun kara farshin man fetur, yayin da Kungiyar Kwadago (NLC) ta shirya tafiya yajin aiki a ranar Laraba 7 ga watan Yuni.

Har ila yau, akwai wasu dalilai da suke nuna cewa yajin aikin kungiyar ba zai ci nasara ba akan cire tallafin.

NLC/Tinubu
CDalilai 5 da Yajin Aikin NLC Akan Cire Tallafin Mai Ba Zai Ci Nasara Ba. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Dalilan sun hada da:

1. Siyasantar da NLC

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

Ana zargin NLC da nuna bangare tun bayan zaban shugabanta, Joe Ajaero.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar ma’aikata, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya halarci taron kungiyar, inda ‘yan Najeriya ke ganin NLC ta kama bangarenta a siyasa.

Peter Obi
Peter Obi ya Halarci Taron Kungiyar Kwadago Ta NLC.Hoto: Reno Omokri.
Asali: Twitter

A ranar Juma’a 2 ga watan Yuni, wani jigo a jam’iyyar APC, Bayo Onanuga ya zargi kungiyar da hada kai da Peter Obi don kawo cikas a mulkin Shugaba Tinubu.

Sannan, wani jigo a jam’iyyar PDP, Reno Omokri shima ya zargin kungiyar da nuna bangarenta wurin hada kai da Jam’iyyar Labour.

2. NLC ta rabu gida biyu

A ranar Asabar 3 ga watan Yuni, an ruwaito cewa NLC ta rabu gida biyu inda Arewaci da Kudu maso Yamma na kungiyar suka yi barazanar fita daga yajin aikin.

3. Hukuncin kotun masana’antu tsakanin FG da ASUU

Kara karanta wannan

Jerin Kungiyoyin Ma’aikata 8 da Za Su Shiga Gagarumin Yajin-Aikin Da NLC Za Ta Shirya

Hukuncin kotun masana’antu akan matsalar kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ya kamata ya zama abin dubawa ga ma’aikata.

Hukuncin kotun akan ‘Ba aiki ba biyan albashi’ da ta tabbatar, yana iya yiyuwa sabuwar gwamnati ta kakaba wannan doka idan NLC ta ci gaba da wannan yajin aiki.

4. Bai kamata yajin aiki ya wuce kwana biyar ba – Barista M.A Lateef

A wani hirarsa da Legit.ng, barista kuma lakcara Misbahu Lateef ya ce duk wani yajin aiki bai kamata ya wuce kwana biyar ba.

Lateef ya ce musabbabin yin yajin aiki shi ne tilasta wa gwamnati ta tattauna da masu yi, a duk lokacin da gwamnati ta fara tattauanawa da kungiyar ya zama dole ma’aikata su dawo bakin aiki.

Amma abin takaici, NLC ta ki tattaunawar yayin da ta ke kokarin tilastawa gwamnati janye hukuncinta

5. Cire tallafin ya shafi kasashen ketare

Rahotanni sun tattaro cewa farashin man fetur ya karu a wasu kasashen ketare kamar su Jamhuriyar Benin bayan cire tallafin mai a Njaeriya inda hakan ke tabbatar da cewa kenan kasar na samar da tallafin man fetur din har kasashen Benin da Niger da kuma Kamaru.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: Kowa Zai Shiga Duhu, Ma’aikatan Lantarki Za Su Bi NLC Zuwa Yajin-Aiki

Hakan na nuna cewa yajin aikin kungiyar ba ana yin sa ne don kishin kasa ba, tunda har kasashen ketare ake taimakawa dalilin cire tallafin.

Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta NLC ta yi ganawar gaggawa da Shugaba Tinubu a Abuja kan cire tallafin mai.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin mai a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.