Hajjin Bana: Sarkin Zazzau Ya Gargadi Masu Zuwa Saudiyya da Goro, Ya Fadi Manyan Illoli
- Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli ya gargadi maniyyatan jihar Kaduna da su guji abin da zai sabawa dokokin kasa mai tsarki
- Sarkin ya yi wannan gargadin ne yayin da ya ke ganawa ta karshe da maniyyatan farko a jihar kafin tafiyarsu kasar Saudiyya
- Ya ce maniyyatan dole su gujewa tafiya da goro kasa mai tsarki saboda ya sabawa dokar kasar, inda ya ce gwamna ko sarki ba za su iya cire su ba
Jihar Kaduna - Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya gargadi maniyyata aikin hajji da su guji zuwa da goro kasa mai tsarki.
Sarkin ya yi wannan gargadin ne yayin da ya ke ganawa da maniyyata jirgin farko a jihar Kaduna.
Sarkin ya ce gwamna ko sarki babu mai iya cire su idan aka kama su a Sudiyya saboda sabawa dokarsu.
“Bayan Shekaru 15 Da Aure”: Matar Aure Ta Koka a Bidiyo Yayin da Mijinta Ya Fada Mata Ita Ba Ajinsa Bace
Ya bayyana yadda Saudiyya ke da tsanani akan dokokinta
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya kamata ku guji tafiya kasa mai tsarki da goro saboda ya sabawa dokokin kasarsu, za su iya kama mutum saboda goro.
"Kuma idan aka kama wani, zai yi wahala gwamna ko sarki ya iya cire mutum a wannan hali.'
Har ila yau ya shawarci maniyyatan da su guji zuwa kasar da duk wani abu da zai iya sabawa dokar kasar don gudun cin mutunci kafin su hau jirgi, cewar Daily Trust.
Sarkin ya gargadi maniyyata da su kaucewa karban kayan wasu
Bamalli ya kuma gargadi maniyyatan da su kaucewa karban jakan mutane don gudun musu sharri musamman masu shigar da kwaya kasa mai tsarki.
A martaninta, mataimakiyar gwamnan jihar, Hadiza Sabuwa Balarabe ta roki maniyyatan jihar da su kasance jakadu nagari ga jihar da ma kasa baki daya yayin da suke kasa mai tsarki.
NAHCON Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Batun Ƙarin Kuɗin Kujerar Hajjin Shekarar 2023
A wani labarin, Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta yi amai ta lashe kan alƙawarin da ta ɗauka cewa maniyyata aikin hajjin bana ba za su biya ko sisi daga cikin ƙarin dala $250 da aka samu ba akan kowace kujerar.
Rahotanni sun tattaro cewa kamfanonin jiragen sama masu jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya sun nemi a kara $250 akan ko wace kujera guda daya saboda rikicin da yaki ci yaki cinyewa a kasar Sudan.
Asali: Legit.ng