Tallafin Fetur: Kowa Zai Shiga Duhu, Ma’aikatan Lantarki Za Su Bi NLC Zuwa Yajin-Aiki

Tallafin Fetur: Kowa Zai Shiga Duhu, Ma’aikatan Lantarki Za Su Bi NLC Zuwa Yajin-Aiki

  • Kungiyar NUEE ta shirya bin NLC zuwa yajin-aikin da ta ke kira a shiga daga ranar Laraba mai zuwa
  • A dalilin janye tsarin tallafin fetur wanda ya jawo tashin farashi a gidajen mai, ‘yan kwadago za su yi bore
  • A wata sanarwa da Sakatare Janar na NUEE ya fitar, ya yi kira ga duka ‘yan kungiyarsa su yi biyayya

Abuja - Kungiyar NUEE ta ma’aikatan wutar lantarki a Najeriya, tayi kira ga ‘ya ‘yanta da su janye aikinsu a fadin kasar a dalilin cire tallafin fetur.

The Cable ta ce Sakatare Janar na rikon kwarya na NUEE, Dominic Igwebike, ya fitar da jawabi ya na mai umartar ‘yan kungiyarsu da su tafi yajin-aiki.

Kungiyar ‘yan kwadago ta kasa watau NLC ta bada sanarwar za ta shiga yajin-aiki a makon nan saboda tashin da fetur ya yi a sakamakon janye tallafi.

Kara karanta wannan

Kamfani Ya Maka Gwamnatin Abba a Kotu, Yana Neman N10bn Saboda Ruguza Otel

Lantarki
Tun can ana wahalar lantarki a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sanarwar Dominic Igwebike

‘Yan kungiyar NUEE za su yi biyyaya ga NLC, su janye aikinsu domin nunawa gwamnati fushinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dominic Igwebike ya nuna su na goyon bayan uwar kungiyar ‘yan kwadago na tafiya yajin-aiki, ya bukaci su fara shirye-shiryen dakatar da zuwa aiki.

"A sakamakon zaman gaggawar da majalisar koli (NEC) ta kungiyar NLC tayi a gidan kwadago a Abuja a ranar 2 ga watan Yuni kan cire tallafin fetur...
Wanda hakan ya jawo mummunan karin wahala ga ‘yan Najeriya tare da hauhawar farashin kaya...
La’akari da wannan, ana bukatar duka shugabanni na matakin kasa da jihohi su fara tattara ‘yan kungiya domin ayi cikakkiyar biyayya ga umarnin nan.
A sani cewa za a janye aiki ne daga karfe 12: 00 na daren Laraba, 7 ga watan Yuni, 2023."

- Dominic Igwebike

Jaridar ta ce idan gwamnatin tarayya ba ta iya shawo kan lamarin tsakanin Litinin da Talata ba, za a wayi garin Laraba babu wuta a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Cire Tallafin Man Fetur Da Tinubu Ya Yi Ya Raba Kan Kungiyar Kwadago

Matsayar 'Yan NUJ

Rahoton Leadership ya bayyana cewa kungiyar ‘yan jarida watau NUJ, ta bada sanarwar cewa za ta shiga zanga-zanga idan ba a janye matakin ba.

Daga hawa mulki, sabon shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nuna gwamnatinsa ba za ta cigaba da biyan tallafin man fetur ba, bai cika kasafin kudi.

Farawa da BismilLah

Tun a makon jiya aka ji labari cewa Bola Tinubu zai fara mulki da zanga-zanga da yajin-aikin ma’aikatan Najeriya, wanda hakan zai iya kawo cikas.

Kara farashin man fetur ne ya jawowa sabon shugaban kasar fushin kungiyar ‘yan kwadago, ana kukan an soke tallafi ba tare da kawo wani tsari ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng