Tarihin Mulkin Najeriya: Jerin Shugabannin Najeriya 16 da Kuma Jihohin da Suka Fito

Tarihin Mulkin Najeriya: Jerin Shugabannin Najeriya 16 da Kuma Jihohin da Suka Fito

Najeriya ta yi zamani da shugabanni 16 tun bayan samun ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 1960 daga hannun Burtaniya.

Wasu daga cikin shugabannin Najeriya sun kasance na soji wadanda suka karbi mulki ta hanyar juyin mulki, yayin da wasu kuma suka kasance shugabannin zaben kato bayan kato na dimokradiyya.

Rahoton da muka tattaro muku ya bayyana shugabannin Najeriya da kuma jihohin da suka fito kamar yadda yake a kafar yanar gizo ta ofishin sakataren gidan gwamnatin tarayya. Haka nan, jaridar Tribune Online ta tattaro jerin shugabannin.

Jerin shugabannin Najeriya da jihohin da suka fito
Tinubu, Buhari, Jonathan, Obasanjo da Abacha | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Muhammadu Buhari/Goodluck Jonathan, (Facebook) and Sani Abacha Twitter/@G_sparking
Asali: UGC

1. Nnamdi Azikiwe

An haifi Nnamdi Benjamin Azikwe a ranar 16 ga Nuwamba 1904, an nada shi Shugaban Najeriya a ranar 1 ga Oktoba, 1963, yana da shekaru 58 a duniya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Bidiyon Buhari Yana Mike Kafa a Gidansa Na Daura Ya Bayyana, Mutane Sun Yi Martani

Ya fito ne daga jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

2. Manjo-Janar Johnson Thomas Aguiyi Ironsi

Manjo Janar Johnson Thomas Aguiyi Ironsi, ya zama shugaban kasan Najeriya a ranar 16 ga Janairu, 1966 ta hanyar juyin mulki, wanda daga baya aka kashe shi bayan watanni shida a karaga a ranar 29 ga Yuli, 1966.

Aguiyi Ironsi dan asalin Umuahia ne a jihar Abia.

3. Janar Yakubu Gowon

Janar Yakubu Gowon shi ne shugaban kasa mafi karancin shekaru a tarihin Najeriya. Ya hau mulki ne bayan rasuwar Aguiyi Ironsi a ranar 1 ga Agusta, 1966, yana da shekaru 31 a duniya.

Shi ma kansa, an yi masa juyin mulki ne a ranar 29 ga Yuli, 1975, kuma asalinsa dan jihar Filato ne

4. Janar Murtala Ramat Mohammed

Ya kasance shugaban kasa na hudu a Najeriya da ya hau mulki a ranar 29 ga Yuli, 1975 a lokacin yana da shekaru 36.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Ba Hafsoshin Tsaro Sabon Salon Yaki da Rashin Tsaro a Najeriya

An kashe shi ne a ranar 13 ga Fabrairu, 1976 kuma shi dan asalin jihar Kano ne.

5. Janar Olusegun Matthew Obasanjo

Obasanjo shi ne dan yankin Kudu maso Yamma na farko da ya mulki Najeriya; daga jihar Ogun, wanda hakan ya yiwu bayan kashe shugabansa Mohammed a ranar 13 ga Fabrairu, 1976.

A lokacin, Obasanjo na da shekaru 38 da haihuwa ya zama shugaban kasa, kuma shi ne shugaban kasa na soja na farko da ya mika wa gwamnatin farar huka kasar a ranar 1 ga Oktoba, 1979.

6. Shehu Usman Aliyu Shagari

Shagari ne ya zama shugaban farar hula na farko a Najeriya a ranar 1 ga Oktoba, 1979, a lokacin yana da shekaru 54 a duniya.

An sake zabensa a shekarar 1983, amma sojoji suka karbi ragamar mulkin kasar a hannunsa a ranar 31 ga Disamba, 1983. Shagari dan asalin jihar Sokoto ne.

7. Manjo-Janar Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani a Ganawar Tinubu da Kungiyar Kwadago

Buhari ya zama shugaban kasa ne bayan nasarar juyin mulkin da ya kai ga hambarar da mulkin Shagari a shekarar 1983, inda ya bar mukin shi ma a ranar 27 ga watan Agustan 1985.

A lokacin, Buhari na da da shekaru 41 da haihuwa kuma dan asalin jihar Katsina ne da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

8. Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Babangida ya zama shugaban kasa na 8 a Najeriya a ranar 27 ga Agusta, 1985, bayan ya hambarar da gwamnatin Buhari a wani juyin mulki da ya yi a lokacin yana da shekaru 44.

Ya mika mulkin daga baya ga Cif Ernest Shonekan a ranar 26 ga watan Agusta, 1993. Babangida dan asalin jihar Neja ne.

9. Cif Ernest Adekunle Oladeinde Shonekan

Shonekan, shi ne shugaban gwamnatin rikon kwarya da aka nada bayan da IBB ya soke zaben ranar 12 ga watan Yunin 1993.

Ya kasance shugaban kasa daga ranar 26 ga Agusta, 1993 zuwa 17 ga Nuwamba, 1993, lokacin da Janar Sani Abacha ya hambarar da shi daga mulki.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Bankin CBN Ya Karyata Labarin Karya Darajar Naira Zuwa N630/$1

Shonekan yana da shekaru 57 a lokacin da hakan ya faru kuma dan asalin jihar Ogun ne.

10. Janar Sani Abacha

Abacha ya hau karagar mulki ne a ranar 17 ga watan Nuwamba, 1993, yana da shekaru 50 a lokacin. Ya shafe kusan shekaru biyar yana mulki. Ya mutu a ranar 8 ga Yuni, 1998.

Marigayi Abacha shi ne shugaban kasan Najeriya na 10 kuma dan asalin jihar Kano ne.

11. Janar Abdulsalami Abubakar

Abdulsalami ya hau karagar mulkin Najeriya bayan rasuwar Abacha a ranar 9 ga watan Yuni 1998, har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 1999, inda ya mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Ya zama shugaban kasa yana da shekaru 55, kuma ya fito ne daga jihar Neja.

12. Olusegun Matthew Obasanjo

Obasanjo ya sake komawa kan karagar mulkin Najeriya shekaru 20 bayan mika da ya yi ga gwamnatin farar hula a shekarar 1979.

Kara karanta wannan

Mazauna Garin Daura Sun Roki ’Yan Najeriya Su Yafe Wa Tsohon Shugaban Kasa Kura-Kuransa

Ya zama shugaban farar hula yana da shekaru 62 kuma ya shafe shekaru 8 yana mulki har zuwa 2007.

Obasanjo dan jihar Ogun ne kamar yadda muka ambata a baya.

13. Umaru Musa Yar'adua

Marigayi Yar'aduwa ya shafe kusan shekaru 3 akan karagar mulki kafin rasuwarsa a ranar 5 ga Mayu, 2010.

An rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2007 a matsayin shugaban Najeriya na 13 a lokacin yana da shekaru 55. Ya fito ne daga jihar Katsina.

14. Dr. Goodluck Ebele Jonathan

Jonathan, a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya karbi mulki bayan rasuwar Yar’adua a watan Mayun 2010, yana da shekaru 52 a lokacin.

Ya fadi a zaben 2015, inda ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari. Jonathan dan asalin jihar Bayelsa ne.

15. Muhammadu Buhari

Buhari ya kasance mafi tsufa da ya taba mulkar Najeriya, wanda ya karbi mulki a karo na biyu yana da shekaru 72.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Nade-Naden Mukamai 7 Ana Tsakiyar Rantsar da Tinubu

Ya zama shugaban Najeriya na 15 a ranar 29 ga Mayun 2015 kuma ya shafe shekaru 8 yana mulki har 29 ga Mayun 2023.

Tsohon shugaban kasar dan jihar Katsina ne da ke Arewa maso Yammacin Najeriya..

16. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Tinubu ya zama shugaban Najeriya na 16 bayan an rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023, yana da shekaru 71 a duniya.

Ya zuwa yanzu, an fara jin tasirin gwamnatin Tinubu, bayan da ya janye tallafin man fetur jim kadan bayan rantsar dashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.