Sabon Gwamna Abba Gida Gida Ya Cigaba da Rusau, Ya Ruguza Ginin Otel a Kano
- Abba Kabir Yusuf ya fara cika alkawarin da ya dauka na karbe filayen gwamnati da aka yi gini a kan su
- Sabon Gwamnan ya bada umarnin rusa duk ginin da aka yi ba a kan ka’ida ba a ko ina a fadin jihar Kano
- Mai girma Gwamnan ya jagoranci ruguje filin sukuwa, a jiya kuma an rusa wani gini da ke cikin Daula otel
Kano - Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya cigaba da abin da ya yi alkawari na karbe filaye gwamnati da aka yi gine-gine a kan su.
A daren Lahadin nan, labari ya zo daga gidan rediyon Freedom cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ruguza gini da aka yi a otel da ake kira Daula.
Sabon Gwamnan ya na ikirarin an yi wadannan gine-gine ne ba a kan ka’ida ba, don haka tun kafin ya dare kan kujera, ya sha alwashin kai su kasa.
Tun a ranar Asabar, sabon Gwamnan ya bada umarnin rusa duk ginin da ya sabawa ka’idar jiha.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dalilin yin rusau
Kamar yadda Sanusi Dawin-Tofa ya fitar da jawabi, gwamnati ba za ta yarda da gini a makarantu, kasuwanni, asibitoci da duk wuraren al’umma ba.
Babban Sakataren yada labaran Gwamnan ya ce yin hakan zai dawo da kimar jihar sannan zai tabbatar da tsari tare da kawata wuri da inganta tsaro.
A gefe guda, wannan ya jawo surutu daga wasu mutane da suke ganin an jawowa jama’a asara.
Da yake magana a shafinsa na Facebook, Ibrahim Adam ya ce Abba K Yusuf ya na ruguza wuraren da suka saba ka’ida ne ba saboda ramuwar gayya ba.
Legit.ng Hausa ta fahimci akwai masu zargin Gwamnan da kokarin yakar Abdullahi Ganduje wanda ya yi mulki sau biyu daga 2015 zuwa 2023.
Matashin ya ce rusa wadannan gine-gine da suka saba ka’ida ya na cikin dalilan da ya sa Kanawa su ka zabi NNPP, ya ce ya yi farin cikin cika alkawarin.
Wani fitaccen 'dan Kwankwasiyya, Salisu Yahaya Hotoro ya rubuta a Facebook:
“Dama mun gaya muku kowa ya siya ya sayi banza idan mutum ya gina kuma ya gina wofi.” - Salisu Yahaya Hotoro
Ahmad Prince Gandujiyya matashi ne mai goyon bayan APC ya ce matakin da Gwamnati ta dauki tayi daidai, ya nuna ba ‘Yan APC aka ba filayen ba.
“Wadanda suka wahala dabam, wadanda suka amfana dabam.”
- Ahmad Prince Gandujiyya
Salihu Tanko Yakasai wanda ya nemi takarar Gwamnan Kano a jam’iyyar PRP ya yi magana a Twitter:
“Muna goyon bayan sa, idan ya gama da manyan plazas kuma ya shiga cikin kasuwa yan tebura da masu talla a titi.
Kowa ya ji a jikin sa. Muna goyon bayan wannan gyara dari bisa dari.”
- Salihu Yakasai
Fada da cikawa
Rahoto ya zo cewa an wayi garin Asabar, gwamnatin Abba ta fara rushe gine-gine a Filin Sukuwa da nufin kwato wuraren da Abdullahi Ganduje ya siyar.
A karshen makon nan ne kuma aka ji Abba Yusuf ya bada sanarwar Gwamnatin jihar Kano ta hana kowace jam’iyya ko wasu lika fasta a jikin bango.
Asali: Legit.ng