Tsadar Man Fetur: FRSC Ta Shawarci 'Yan Najeriya Su Koma Amfani Da Kekuna, Ta Fadi Dalilai
- Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Bayelsa ta shawarci ‘yan Najeriya da su koma amfani da kekuna wajen harkokin sufuri
- Kwamandan FRSC na jihar, Usman Ibrahim ne ya yi kiran, inda ya ce amfani da kekuna yana da arha, kuma yana da fa'ida ga lafiyar ɗan adam
- Ya ce ƙasashen da suka ci gaba suna amfani da keke wajen zirga-zirgar domin kiyaye muhalli ta hanyar rage yawan fitar da iskar da ke gurɓata yanayi
Bayelsa - Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Bayelsa, ta shawarci ‘yan Najeriya da su koma amfani da keke a matsayin hanyar sufuri a daidai lokacin da farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi.
Kwamandan hukumar FRSC na Bayelsa, Usman Ibrahim, ne ya ba da wannan shawarar a yayin taron wayar da kan jama’a don tunawa da ranar keke ta duniya ta bana, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shehu Sani Ya Yi Wa APC Wankin Babban Bargo a Kaduna, Ya Bayyana Wani Bangare Na Musamman Da Jami'yyar Ta Gaza
Kwamandan FRSC ya ce keke na da amfani ga lafiyar ɗan adam
Ibrahim ya ce, amfani da keke ya fi sauƙi kuma yana da matuƙar amfani ga lafiyar dan Adam.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Ibrahim, wanda mataimakin kwamandan rundunar FRSC a jihar, Oiwoja Alagoa ya wakilta, ya ce lokaci ya yi da za a sake dawo da tsarin sufurin keke, wanda ya taimakawa ɗan adam na tsawon shekaru masu yawa.
Ƙasashen da suka ci gaba na amfani da keke wajen motsa jiki
Kwamandan shiyyar daga nan ya jagoranci tawagar masu keke da suka haɗa da jami'an hukumar ta FRSC, matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), da wasu kwararru a yayin zuwa zagayen na wayar da kan jama’a.
Kwamandan ya kuma bayyana cewa ƙasashe irin su Denmark, China, Poland da sauransu galibi suna amfani da keke ne wajen motsa jiki da makamantansu.
Gwamnan Arewa Ya Ɗau Zafi, Ya Ce Zai Soke Lasisin Mallakar Duk Gidan Man da Ya Ɓoye Fetur Ko Ya Kara Farashi
Ya ƙara da cewa keken, baya ga arha da yake da ita fiye da sauran abababen hawa, yana da amfani sosai wajen taimakwa lafiyar jikin ɗan adam da ma muhallinsa.
Ya bayyana cewa, saboda ɗumbin alfanun da keke yake da shi ne ya sa majalisar ɗinkin duniya a shekarar 2017, ta ayyana ranar 3 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar tunawa da kekuna ta duniya.
Ya ce:
“Ana amfani da keke wajen kiyaye yanayi, saboda ba ya fitar da iskar da ke gurɓata yanayi, sannan yana taimakawa wajen rage cunkoso a hanyoyi.”
Ya kuma ce ƙasashen da suka ci gaba tuni suka karɓi tsarin sufuri na kekuna, musamman don kare lafiyar jama'a da kuma rage yawan fitar da sinadarin da ke gurɓata iska da sauran ababen hawa ke fitarwa.
A saboda da haka ne ya shawarci 'yan Najeriya da su rungumi amfani da kekunan don inganta lafiyarsu da kuma tattala kudadensu.
A cewarsa:
"Muna son mutanenmu su dawo kan tsarin, saboda hawan keke yana da kyau ga jiki, muhalli kuma yana taimakawa tattalin arziƙin mai amfani da shi.”
Jaridar Leadership ta ruwaito kwamandan FRSC na jihar Kwara, Fredrick Ogidan, ma yana kira ga 'yan jihar da su rungumi amfani da kekuna don inganta lafiyar jikinsu.
Alfanun cire tallafin man fetur 5 da ya kamata 'yan Najeriya su sani
A wani labarin mai alaƙa da cire tallafin na man fetur, Legit.ng ta kawo muku wasu alfanu 5 na cire tallafin man fetur da kowane ɗan Najeriya ya kamata ya sani.
Tallafin man fetur dai wani nau'i ne na tallafi da gwamnati ke biyan wasu kuɗaɗe kai tsaye zuwa ga kamfanonin mai domin su sauƙaƙa farashin man fetur ga 'yan ƙasa.
Asali: Legit.ng