An Kama Wani Kasurgumin Mai Satar Wayoyi Yana Sharar Bacci a Coci
- Wani shahararren mai satar wayoyi, Saheed Abioye wanda aka fi sani da Anini, ya shiga hannun yan sanda
- Anini ya ziyarci wani coci a garin Osogbo da nufin sace wayoyin masu bauta amma sai ya kama sharar bacci
- Bayan ya farka a lokacin da an riga an gama bauta har mutane sun watse sai ya kama hanyar gida, amma ya hadu da bacin rana
Osun - Rundunar yan sandan jihar Osun ta kama wani direba mazaunin Ibadan da ke jihar Oyo, Saheed Abioye wanda aka fi sani da Anini.
An tattaro cewa an kama wanda ake zargin ne yayin da yake hanyarsa ta komawa gida bayan kokarinsa na sace wayoyin salula a wani cocin Osogbo ya ci tura, jaridar Punch ta rahoto.
Ya ziyarci coci da nufin sace wayoyi
Shehu Sani Ya Yi Wa APC Wankin Babban Bargo a Kaduna, Ya Bayyana Wani Bangare Na Musamman Da Jami'yyar Ta Gaza
Da aka gurfanar da shi a hedkwatar yan sanda, mutumin wanda ke da haihuwar 'da daya ya bayyana cewa ya dawo Osogbo daga Ibadan ne don duba yaronsa wanda ke zama da danginsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa, kafin ya duba dan nasa, ya yanke shawarar ziyartan wani coci a yankin Alekuwodo da ke jihar Osun, inda ake addu'an dare, da niyan satar wayoyin wasu masu bauta.
Ya ce:
"Na isa cocin da misalin karfe 10:45 na dare sannan na zauna, ina jiran samun damar sace wayoyin mutanen da za su so sa chaji a bayan cocin.
"Abun takaici, na gaza sace komai a wannan rana saboda bacci ya dauke ni jim kadan bayan an fara addu'an daren kuma ban tashi ba har sai da misalin karfe 3:00 na tsakar dare.
"Zuwa lokacin da na tashi, an gama addu'an daren kuma tuni mutane suka fara tafiya gida, don haka na bar harabar cocin. Ban yi nasarar sace komai ba.
Ya cigaba da cewa:
"Lokacin da na isa yankin Alekuwodo, kafin kasuwar Akindeko, sai na ga motar fatrol na yan sanda da wasu jami'an da ke yaki da kungiyar asiri daga Dugbe (hadkwata, Osogbo). Sun dakatar da ni sannan suka nemi sanin me nake sauke da shi sai na amsa masu da jakana da katin shaida. Sun chaje ni amma basu samu wani mugun abu ba.
"Daga bisani sai suka dauke ni zuwa cocin don tabbatar da ko da gaske daga nan nake. Lokacin da suka tambayi faston, ya ce bai ganni ba a cocin, don haka suka mayar da ni ofishin yan sandan Dugbe.
"Daga baya, aka dauki bidiyona sannan aka tura sauran ofishohin yan sandan sannan wasu jami'ai, wadanda suka kama ni a baya suka gane ni a matsayin shahararren mai sace-sacen wayoyi. Bana satar motoci, babura da sauransu sai wayoyi kawai."
Abioye ya yi ikirarin sacewa da siyar da wayoyi sama da guda 18 daga bangarori daban-daban na jihar.
Rundunar yan sanda ta yi martani
Kakakin rundunar yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin bayan kammala bincike.
Yan bindinga sun kai hari Abuja, sun sace mutum hudu
A wani labarin, mun ji cewa yan bindiga dauke da muggan makamai a safiyar ranar Asabar, sun farmaki unguwar Mashafa a cikin Mpape a birnin tarayya Abuja.
Maharan sun yi awon da gaba da mutum huɗu, a farmakin da suka kai unguwar wanda suka shafe kusan sa'a daya.
Asali: Legit.ng