Shugaban NNPC Kyari, Ya Bayyana Babban Dalilin Da Ya Sa Dole a Cire Tallafin Man Fetur
- Babban manajan daraktan NNPC, Mele Kyari ya bayyana cewa Gwamantin Tarayya ba za ta iya ci-gaba da biyan kuɗaɗen tallafin man fetur ba
- Ya ce yanzu haka NNPC na bin Gwamnatin Tarayya bashin kuɗaɗe da suka kai tiriliyon biyu da ɗigo takwas (N2.8t) kuma har yanzu gwamnatin ta gaza biya
- Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin raba kayayyakin tallafi ga 'yan Najeriya domin rage tasirin wahalhalun da cire tallafin man fetur ɗin zai haifar
Babban manajan daraktan kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya ce babu gudu babu ja da baya kan batun cire tallafin man fetur saboda Najeriya ba za ta iya ci-gaba da biyan tallafin ba.
Kyari ya zanta da manema labarai ne bayan ganawa da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ranar Alhamis, a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa dake Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Matakin Tinubu na shan suka
Shugaba Bola Ahmed Tinubu jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya na 16, ya sanar da cire tallafin man fetur a hukumance.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai wannan matakin nasa na shan suka daga 'yan Najeriya saboda tsadar rayuwa da ta addabesu.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, a ranar Laraba, ya ce cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ya haifar da ƙalubale sosai ga ‘yan Najeriya musamman ma waɗanda suke a jihohi.
Sai dai Mele Kyari ya ce kuɗaɗen tallafin da ake bin gwamnati sun yi yawa, yana mai jaddada cewa ƙasar har yanzu ta gaza biyan NNPC kuɗaɗen da take kashewa kan tallafin man fetur.
NNPC na bin Gwamnatin Tarayya bashi, In Ji Kyari
Sai dai kuma ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin bayar da tallafi ga al'umma domin daƙile tasirin wannan mataki da gwamnati ta ɗauka.
Kyari ya ce a shekarar 2022, gwamnati ta biya kuɗaɗen na tallafi, amma a shekarar 2023, ko sisi ba a bayar ba da sunan tallafi.
A rahoton Guardian, Kyari ya ƙara da cewa yanzu haka suna bin gwamnati bashin kuɗaɗen tallafi da suka kai tiriliyon biyu da ɗigo takwas (N2.8t).
Dan majalisa ya koma hawa keke saboda da tsadar fetur
A wani labarin mai alaƙa da janye tallafin mai, kun ji labarin wani ɗan majalisan jihar Adamawa da ya ajiye motarsa ya koma hawa keke saboda tsadar man fetur.
Ɗan majalisar yace wannan nau'ine na zanga-zangar nuna ƙin amincewa da cire tallafin man da gwamnatin tarayya ta yi.
Asali: Legit.ng