Zanga-Zanga Ta Barke a Jihar Edo Kan Tashin Farashin Man Fetur
- Mutanen jihar Edo sun fara toshe hanyoyi suna zanga-zangar adawa da ƙara farashin litar man Fetur
- Shugaban tawagar masu zanga-zangar ya ce sun fito kan Tituna ne domin jawo hankalin shugaban ƙasa, Tinubu, ya ɗauki mataki
- A ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, aka wayi gari litar mai ta koma sama da N500 a gidajen man NNPCL
Abuja - Dandazon mazauna jihar Edo sun toshe babban titin Benin-Lagos da wasu yankuna a cikin birnin Benin biyo bayan ƙara farashin litar man Fetur (PMS), kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Masu zanga-zangar nuna fushi kan lamarin, wanda mafi yawa mambohin ƙungiyar fararen hula ta jihar Edo (EDOCSO) sun nemi mahukunta su gaggauta soke ƙarin da suka yi.
Tawagar mutanen na ɗauke da allunan da aka yi rubutu daban-daban kamar, "Yan Najeriya ba zasu sayi litar mai N520 ba,";"Ba zamu lamurci sayen fetur N520 ba a dawo da farashin N210."
Wasu allunan kuma an rubuta, "Ya zama tilas farashin Fetur ya dawo N210 har ƙarshen watan Yuli," kuma a cewar masu zanga-zanga kalubale sun yi wa yan Najeriya yawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan zanga-zanga da ta barke ta haddasa cunkoson ababen hawa a birnin Benin, lamarin da ya tilastawa matafiya taka sayyadar ƙafarsu zuwa wuraren da suka nufa.
Menene manufar masu zanga-zanga?
Da yake zantawa da yan jarida, kodinetan ƙungiyar EDOCSO, Omobude Agho, ya ce sun tsiri wannan zanga-zanga ne domin jawo hankalin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce:
"Muna zanga-zanga ne saboda ƙara farashin litar man fetur wanda ya fara daga jiya, 'yan kasuwa sun tashi farashi daga N210 zuwa sama da N500."
"Mun kaɗu da muka ga har kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya ƙara farashin zuwa sama da N500, saboda haka muna ganin kamar wani shiri ake na ganin bayan yan Najeriya ko tura mu ƙabari."
Bayan Rantsar da Sabon Gwamna, Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jami'an Tsaro da Wasu 17 a Jihar Arewa
Ya ƙara da cewa sun fara wannan zanga-zanga ne a matakin cikin gida amma idan zuwa Jumu'a gwamnati ba ta saita lamarin ba, zanga-zangar zata ƙara yaɗuwa, Punch ta tattaro.
Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakaki
A wani labarin kuma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban majalisat dattawa da kakakin majalisar wakilan tarayya a Aso Villa.
Manyan shugabannin sun fara tattaunawa da misalin karfe 2 da wasu 'yan mintuna na rana bayan Tinubu ya fito zama da hafsoshin tsaro.
Asali: Legit.ng