Yadda Ma’aikatu Suka Yi Bindiga da Naira Tiriliyan 3.8 a Karkashin Mulkin Buhari
- Akwai SWV a kasafin kudi wanda ke ba ma’aikatu damar kashe dukiya idan an shiga matsin lamba
- Majalisar dattawa tayi bincike ta gano yadda aka rika amfani da wannan tsari wajen facaka da kudi
- Kwamitin Matthew Urhoghide ya ce ta haka aka tafka badakalar N3.8tr tsakanin shekarar 2017 da 2021
Abuja - Ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya da-dama sun karkatar da Naira Tiriliyan 3.8 da suka shigo hannunsu ta karkashin SWV.
Wani bncike da majalisar dattawa ta gudanar a kan inda aka kai kason SWV na shekaru hudu ya bankado wannan asirin, Daily Trust ta fitar da rahoton.
Kwamitin da ke kula da baitul-mali a majalisar dattawa ya yi bincike kan Naira tiriliyan 5 da ya shiga hannun ma’aikatu 207 tsakanin 2017 da 2021.
Sanata Matthew Urhoghide da ‘yan kwamitinsa sun gayyaci ma’aikatu 207, amma 119 kadai su ka amsa. A ranar Larabar nan su ka gabatar da rahotonsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake mika rahoton binciken da suka yi, Urhoghide ya ce ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati su na karbar SWV ba da sanin ‘yan majalisa ba.
Sanata Urhoghide ya nuna akwai ma’aikatun da ba su nemi kudin nan a hukumance ba, amma kurum ofishin Akanta Janar na kasa ya aika masu da miliyoyi.
An yi amfani da shugaban kasa
Idan kuwa aka samu shugaban kasa ya amince da rokon kudin, binciken majalisar ya nuna ma’aikatan su na karkatar da kudin ayi wasu abubuwa dabam.
A cewar Sanatan, MDA su ka karbi kudi da sunan ayyukan da tuni an cusa su cikin kasafin kudi.
Premium Times ta ce binciken ya nuna an rika karbar biliyoyi da sunan za a cike gibin albashi bayan an tanadi IPPIS, kuma an ware kudin biyan ma’aikata.
Ma’aikatun da suka rika yin wannan facaka sun ki amsa gayyatar kwamitin majalisar da gan-gan, watakila ba su da bayanin da zai gamsar da Sanatocin.
Ma'aikatun da ake zargi
Daga cikin inda ake zargin an tafka badakalar akwai ofishin Akanta Janar da ma’aikatun cikin gida, harkokin waje, kudi, sufuri, kiwon lafiya da tsaro.
Ana zargin ma’aikatun ayyuka da gidaje, labarai da al’adu, harkokin ‘yan sanda, ma’adanai, matasa da wasanni, harkokin jirgin sama da na man fetur.
Haka abin yake a hukumomin NAFDAC, NSCDC, FERMA, NEMA, DMO, NAHCON, NEDC, NIA, NHIS, NACA, NECO da wasu dinbin ma’aikatan gwamnati.
Albashi ya makale
Ma'aikatan gwamnatin tarayya da jami'an tsaro ba zasu samu albashin watan Mayu a kan lokaci ba, a tsakiyar makon nan mu ka fitar da wannan rahoto.
Wasu daga cikin ma'aikatan gwamnati sun ce har yanzu shiru, ba a biya su albashin watan Mayu ba. Amma wasu bayanai sun nuna dalilin jinkirin nan.
Asali: Legit.ng