Ganawar FG Da Kungiyar NLC Kan Cire Tallafin Man Fetur Ta Tashi Baran-Baran

Ganawar FG Da Kungiyar NLC Kan Cire Tallafin Man Fetur Ta Tashi Baran-Baran

  • An fara tattaunawa tsakanin gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu da kungiyar kwadago kan cire tallafin man fetur
  • A zaman farko an tashi baran-baran ba tare da an cimma wata matsaya guda ba domin dai kungiyar NLC ta nuna lallai a soke sabuwar farashin mai kafin a fara tattaunawa
  • Kamfanin man fetur din Najeriya (NNPCL) ta sanar da sabon farashin da take so gidajen manta a fadin kasar su dunga siyar da kowace litar mai

Abuja - Ganawar da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) kan cire tallafin man fetur ya tashi ba tare da an cimma wata matsaya guda ba, Channels TV ta rahoto.

An fara ganawar ne da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Laraba, 31 ga watan Mayu a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Tinubu Na Ganawar Sirri Da Oshiomhole, NLC Da TUC

Kakakin Tinubu, Dele Alake yana bayani bayan taro kan cire tallafin mai
Yanzu Yanzu: Taron FG Da Kungiyar NLC Kan Cire Tallafin Man Fetur Ya Tashi Baran-Baran Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Wakilan gwamnatin tarayya sun hada da Dele Alake, kakakin shugaban kasa Bola Tinubu da shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari.

Sauran jami'an gwamnatin da suka hallara sun hada da gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kungiyar kwadagon ta samu wakilcin shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero da shugaban TUC, Festus Osifo.

Kungiyar kwadago ta bukaci FG ta mayar da farashin yadda yake a baya kafin su tattauna

Bayan shafe awanni masu yawa suna tattaunawa da gwamnatin tarayya, kungiyar kwadago ta bukaci cewa gwamnatin ta mayar da farashin man yadda yake kafin su fara tattaunawa a tsakaninsu.

Shugaban kungiyar kwadagon na kasa, Joe Ajaero, wanda ya caccaki cire tallafin ya bayyana cewa a koma yadda ake kafin fara tattaunawa da NLC domin kare ma'aikatan Najeriya da kuma samar da karin mafita masu dorewa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kungiyar Kwadago Ta Dau Zafi, Ta Yi Watsi Da Sabon Farashin Man Fetur

Kungiyar ta NLC ta dage cewa gwamnatin tarayya ta shiga kowace tattaunawa ba koda a kan matakan ragewa yan Najeriya radadi ne, don haka basu amince da sanarwar ta baya-bayan nan ba.

Kungiyar ta ce ta yanke shawarar sake zama da mambobinta domin sanin mataki na gaba da za su dauka.

Za mu cimma matsaya a tarukan gaba, Kakakin Tinubu

Sabanin haka, Alake ya bayyana taron a matsayin mai girma, inda ya kara da cewa za a ci gaba da tattaunawa. Ya nuna yakinin cewa za a cimma matsaya mai ma'ana tsakanin bangarorin biyu a taron da za su yi na gaba, rahoton Daily Trust.

Kungiyar NLC ta yi watsi da sabon farashin man fetur

A baya mun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa ta yi watsi da sabon farashin da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayar.

Kamfanin man fetur din ya ba gidajensa a fadin kasar umurnin siyar da fetur tsakanin N480 da N570.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng