Za'a Samu Jinkirin Albashi Ga Ma'aikatan FG da Jami'an Tsaro a Watan Mayu
- Bayanai sun nuna za'a samu tsaiko kafin mahukunta su biya ma'aikatan gwamnatin tarayya Albashin watan Mayu
- Wannan dai ya samu asali ne daga jinkirin CBN na amincewa ma'aikatu su biya albashi ga ma'aikatansu
- Wata majiya a ofishin shugaban ma'aikatan Najeriya ta ce umarni ne daga sama na a rufe asusun ma'aikatu da hukumomi
Abuja - Ma'aikatan Najeriya da ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya zasu gamu da ɗan jinkiri gabannin a biya su albashin watan Mayu, 2023, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wakilin jaridar ya tattaro cewa za'a samu ɗan tsaikon biyan albashin ne saboda har kawo yanzu babban bankin Najeriya (CBN) bai amincewa ma'aikatu, sashi-sashi da hukumomi su cire kuɗi ba.
Tun da farko, wasu ma'aikatan gwamnatin tarayya sun tabbatarwa wakilin jaridar cewa har yanzun ba'a biya su albashin watan Mayu, 2023 ba.
Jerin Gwamnonin APC, PDP, LP Da Suka Kulle Asusun Ajiya a Jihohin Su Daga Shiga Ofis Da Dalilan Yin Hakan
A wata sanarwa da aka aike wa ma'aikatan filayen jirgin sama daga mahukunta, hukumar ta gaya musu wannan tsaikon rashin biyan albashin ya shafi baki ɗaya ma'aikata harda jami'an tsaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwan mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin manajan sashin gudanarwa, Oluwasola Awe, ta ce:
"Muna sanarwa kafatanin ma'aikata cewa mun ɗora neman izinin biyan albashi kuma a halin yanzu muna jiran sahalewar babban bankin Najeriya na cire kuɗin."
"FAAN ta samu labarin cewa za'a samu tsaiko wajen biyan albashin watan Mayu sakamakon wata 'yar matsala da ta taɓa Fotal ɗin CBN."
"Saboda haka ku sani, wannan matsalar ba FAAN kaɗai ta shafa ba, sauran ma'aikatu harda rundunar soji da sauran hukumomin tsaro suna fama da wannan jinkirin."
Da yake tabbatar da haka, wata majiya daga ofishin shugaban ma'aikatan tarayya ta ce:
"Eh gaskiya ne, an samu umarnin garƙame asusun ma'aikatu daga sama, shiyasa CBN ya gaza cire kudaɗen daga Asusu kuma hakan ya haifar da jinkirin biyan albashi."
Gwamnatin Tinubu Ta Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya
A wani labarin kuma Najeriya ta cire tallafin man Fetur yayin da aka wayi gari kamfanin mai na ƙasa NNPC Limited ya ƙara farashi kan kowace lita.
Da safiyar ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, kamfanin NNPC Limited ya sauya farashin Man Fetur zuwa N537 kan kowace lita ɗaya a Abuja .
Asali: Legit.ng