Dalilin Da Ya Sa ‘Yan Kasuwa Suka Kara Farashin Man Fetur Bayan Jawabin Shugaba Tinubu

Dalilin Da Ya Sa ‘Yan Kasuwa Suka Kara Farashin Man Fetur Bayan Jawabin Shugaba Tinubu

  • An bayyana dalilin tashin farashin man fetur da ya faru babu tsammani a ranar rantsuwar shugaban ƙasa Tinubu
  • Tun bayan rantsar da shugaba Tinubu, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a duk faɗin Najeriya
  • Layin man fetur ya dawo a gidajen mai, inda wasu da yawa daga cikinsu ke siyar da man akan kuɗaɗe har N700 a kowace lita

Wani ɗan kasuwar man fetur ya bayyana dalilin da ya sa aka sami tashin gwauron zabi kan farashin man fetur a faɗin Najeriya, tun bayan jawabin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi a wajen bikin rantsar da shi.

Za a iya tuna cewa, jim kaɗan bayan da shugaba Tinubu ya bayyana cewa babu bayanin tallafin man fetur a gwamnatinsa, ‘yan Najeriya suka fara rurrumar siyan man fetur saboda da fargabar abinda ka iya biyowa baya.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin APC, PDP, LP Da Suka Kulle Asusun Ajiya a Jihohin Su Daga Shiga Ofis Da Dalilan Yin Hakan

Dalilin tashin farashin man fetur a Najeriya
An bayyana dalilin tashin farashin man fetur tun bayan maganar Tinubu kan tallafi. Hoto: NOA, NAN
Asali: UGC

Lamarin ya sanya akasarin gidajen man ƙasar nan ƙara farashin man har zuwa sama da naira 500 a kan kowace lita.

Hakan ya haifar da dogayen layuka a gidajen mai da kuma sabbaba ƙarin farashin sufuri musamman a manyan biranen Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi sakamakon tsananin bukata

A zantawarsa da Legit.ng dangane da hauhawar farashin man fetur da aka samu, Jude Awaliabe, mamba a ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) reshen jihar Legas, ya bayyana dalilin hauhawar farashin.

Ya ce an samu hauhawar farashin man ne sakamakon batun nan na kasuwa, na ƙaruwar darajar abu a lokacin da buƙatarsa ta ƙaru.

A kalamansa:

“Dukkanmu mun san yadda kasuwa ke tafiya. Da zarar ana tsananin buƙatar abu, dole ne farashin ya ɗaga, haka nan ma kuma akasin hakan. Abinda ya faru a ranar Litinin, shi ne, wasu gidajen mai sun lura da wata damar samun kuɗaɗe daga hannun al'umma, sai kawai suka yi amfani da ita."

Kara karanta wannan

Farashin Fetur Ya Kai N600 Zuwa N1200 a Wurare a Ranar Farkon Tinubu a Ofis

"Wannan a wurina ba adalci bane, ganin cewa man da ke jibge a gidajen mansu, mai ne da gwamnati ta riga ta ba da tallafi a kai."

Awaliabe ya ƙara da cewa duk da cewa gwamnatin tarayya tun a lokacin baya ta bayyana aniyarta ta cire tallafin man fetur, ya ce ta gaza wajen daukar matakan daƙile tasirin abinda hakan zai jawowa ‘yan Najeriya.

Yan takara sun sha alwashin cire tallafin man a baya

Shekaru da dama, ana yawan tafka muhawara kan batun tallafin man fetur, wanda ake ganin gwamnati na ɓarnatar da kaso mai tsoka na kasafin kuɗin ƙasar wajen biyan 'yan kasuwar man na fetur ɗin.

Duka manyan ‘yan takarar shugabancin Najeriya a zaɓen da ya gabata, sun bayyana cewa za su cire tallafin man idan suka ci zaɓe, wato idan suka zama shugaban ƙasa kenan.

Gwamnati ta tabbatar da cire tallafin man fetur

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗau Zafi, Ya Ce Zai Soke Lasisin Mallakar Duk Gidan Man da Ya Ɓoye Fetur Ko Ya Kara Farashi

A wani labarin namu na baya, kun ji cewa ta tabbata gwamnatin Najeriya ta zare hannunta daga batun tallafin man fetur.

Hakan dai ya tabbata ne biyo bayan sanarwar da kamfanin NNPC ya fitar na ɗaga farashin man fetur ɗin zuwa N537 duk lita ɗaya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng