'Yan Najeriya su Shirya, NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur a Duk Gidajen Mai da Ke Karkashinsa
- Kamfanin man fetur a Najeriya ya kara farashin litar mai a fadin kasar sakamakon cire tallafi da gwamnati ta yi
- A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafinsa na Twitter, ya ce ya kara farashin ne don yin daidai da halin da ake ciki
- Kamfanin har ila yau ya roki 'yan Najeriya da su yi hakuri akan wahalhalun da hakan zai iya haifarwa dalilin karin farashin
Abuja – Kamfanin man fetur a Najeriya, NNPC ya tabbatar da kara farashin litar man fetur a gidajen mayin da suke karkashinsa.
A wata sanarwa ta kamfanin ya fitar a ranar Laraba 31 ga watan Mayu ta bakin kakakin kamfanin, Garba Deen Muhammad ya ce karin farashin ya yi daidai da yadda tsarin kasuwa yake a yanzu.
Sanarwar ta ce farashin a gidajen mai na gwamnati yanzu zai bambanta saboda ya yi daidai da tsarin ‘yan kasuwa.
Kamfanin ya nemi afuwan 'yan Najeriya
TheCable ta tattaro cewa, kamfanin ya roki 'yan Najeriya afuwa akan irin wahalhalun da karin farashin zai iya haifarwa ga mutanen kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar sanarwar:
“Kamfanin man fetur, NNPC na sanar da kwastominmu cewa mun sauya farashin litar mai a gidajen mai dake karkashinmu, saboda ya yi daidai da halin da ake ciki.
“A kokarinmu na kawo muku ingantaccen tsari kamar yadda aka san mu, ya kamata ku sani cewa farashin zai ci gaba da sauyawa saboda ya yi daidai da tsarin kasuwa."
Sanarwar ta kara da cewa:
“Muna tabbatar muku cewa kamfaninmu ya shirya tsab don tabbatar da wadatuwar man a fadin kasar.
“Muna mai baku hakuri da neman afuwa kan wahalhalun da hakan zai iya haifarwa.”
Tinubu ya sanar da cire tallafin mai
Karin farashin man fetur din na zuwa ne bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar cewa gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur a kasar yayin bikin rantsar da shi.
NNPC Ya Tura Sako Ga ’Yan Najeriya Bayan Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur
A wani labarin, Kamfanin man fetur, NNPC ya goyi bayan cire tallafin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi yayin rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.
Shugaba Tinubu ya ce ya cire tallafin ne saboda kasafin kudi na shekarar 2023 bai ba da gurbin tallafin mai din ba.
Asali: Legit.ng