Daga Fara Mulki, Korafi Ya Fara Fitowa, Abba Gida-Gida Ya Koka Kan Karancin Ruwa a Kano
- Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya koka kan yadda ya ga matsalar ruwa ta yi katutu a jihar
- Abba Yusuf ya bayyana haka ne yayin kai ziyara a kukumar tace ruwa ta Challawa a ranar Talata 30 ga watan Mayu
- Gwamnan ya bai wa hukumar kula da ruwan sha ta jihar mako guda su rubuto bukatunsu don shawo kan matsalar
Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya saka dokar ta baci akan karancin ruwa da jihar ke fama da shi.
Gwamnan ya bai wa ma’akatar ruwa ta jihar Kano mako daya da ta tabbatar ta kawo duk wasu bukatunta don dakile matsalar ruwan sha a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kai ziyarar gani da ido wurin tace ruwa na Challawa a ranar Talata 39 ga watan Mayu.
Ya ce matsalar ruwan sha na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta ba kulawa na musamman don kawo karshen matsalar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan ya nuna bacin ransa akan matsalar ruwa
A yayin ziyarar, gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa ganin yadda wurin tace ruwan ya lalace inda ya ba da tabbacin cewa matsalar ruwan sha za ta zama tarihi nan ba da jimawa ba.
Da yake karin haske, Daraktan hukumar tace ruwan ta Challawa, Sakabu Lawal ya bayyana cewa biyu daga cikin shida na injunan tura ruwan ne suke aiki.
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna jihar sun koka kan yadda matsalar ruwa ya yi katutu inda yake taba harkokinsu na yau da kullum.
Abba Gida Gida ya ce zai cika dukkan alkawuran da ya dauka
Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya na cewa gwamnatinsa za ta cika dukkan alkawuran da ta dauka, inda ya bukaci ‘yan jihar da su bashi cikakken goyon baya.
Har ila yau, matsalar ruwan sha ba iya birane kawai ya tsaya ba har ma da sauran kauyuka da suke keyawa da birnin Kano.
Kananan ’Yan Kasuwa Sun More, Abba Gida-Gida Ya Yafe Musu Biyan Haraji
A wani labarin, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce masu kananan sana'o'i ba za suna biyan haraji ba a jihar.
Gwamnan ya bayyana wadanda suke samun kudi kasa da N30,000 ba za su biya kudin haraji ba saboda yanayin da ake ciki.
Asali: Legit.ng