Abba Gida Gida Ya Dumfari Aiki, Ya Fitar da Jerin Mukaman Farko a Gwamnatinsa
- Abba Kabir Yusuf ya nada Sakataren Gwamnati da sauran manyan mukarraban Gwamnatinsa
- Sabon gwamnan jihar Kano ya zabi Shehu Wada Sagagi a matsayin Shugaban ma’aikatan fada
- An canza Shugabannin hukumar da ke kula da jin dadi da walwalar alhazan jihar Kano a ranar farko
Kano - Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda mutane su ka fi sani da Abba Gida-Gida, ya yi nadin mukaman farko a ofis.
A wata sanarwa da ta fito ta ofishin Sakataren yada labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamnan Kano ya sanar da mukarrabansa.
Jawabin ya tabbatar da tsohon shugaban hukumar TETFund ta kasa, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya zama sabon sakataren gwamnatin Kano.
Tsohon shugaban PDP, Hon. Shehu Wada Sagagi ya zama shugaban ma’aikatan fada.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan Kano Ya Kori Shugaban Hukumar Alhazai, Sheikh Pakistan, Ɗiyar Sheikh Ja'afar Da Wasu, Ya Naɗa Sabbi
Dr. Farouq Kurawa ya zama babban sakataren Gwamna watau PPS yayin da Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo ya rike kujerar da ya ke a kai.
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya cigaba a matsayin babban sakataren yada labarai.
Rahoton Daily Trust ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya zabi wadannan mutane ne bayan la’akari da kokari da amanarsu.
Hukumar Alhazai
Ana haka ne kuma sai ga rahoto cewa Mai girma Gwamnan ya nada shugabannin da za su kula da hukumar kula da jin dadin Alhazai a jihar.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, an ji Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Yusuf Lawan a matsayin sabon shugaba.
Laminu Rabi’u zai rike matsayin babban sakatare na hukumar jin dadi da walwalar alhazan.
Sauran shugabannin sun hada da; Shiek Abbas Abubakar Daneji, Shiek Shehi Shehi Maihula, Amb. Munir Lawan da Shiek Isma'il Mangu.
Daily Nigerian ta ce ragowar su ne Hajia Aishatu Munir Matawalle da Dr. Sani Ashir.
Ganduje a Abuja
A rahoton da mu ka fitar a baya, ba a kyale Dr. Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsah Ganduje zama tare manyan baki a Eagle Square.
Tsohon Gwamnan na Kano bai da takardar gayyatar da zai shiga sashen baki masu alfarma, saboda haka ya zauna cikin gama-garin jama'a.
Asali: Legit.ng