“Kwadayin Masu Ciki Sai Su”: Mai Ciki Ta Kona Miyan Abincinta, Ta Sharbi Abun ta

“Kwadayin Masu Ciki Sai Su”: Mai Ciki Ta Kona Miyan Abincinta, Ta Sharbi Abun ta

  • Wata mai ciki ta baiwa mutane mamaki a soshiyal midiya bayan ta wallafa wani al'amari da ya ritsa da iya a baya-bayn nan
  • A cewar mai shirin zama uwar, tana tsaka da bacci da tsakar dare sai ta ji kamar an tashe ta daga nan kuma sai ta fara jin sha'awar konannen abinci
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon inda mata da dama suka bayyana irin nasu kwadayin da suka yi lokacin da suke da ciki

Wata mata mai juna biyu ta haddasa cece-kuce a intanet bayan ta wallafa wani bidiyo a dandalin TikTok.

A bidiyon, an gano mai shirin zama uwar tana sharbar konannen miya a cikin wani faranti inda ta mayar da hankalinta kacokan a kai kamar wani abun azo a gani.

Kara karanta wannan

"Samun Kwanciyar Aure Mai Kyau Ne Ya Sa Na Yi Tsawon Rai", Tsohuwa Mai Shekaru 102

Mai ciki tana shan konannen miya
“Kwadayin Masu Ciki Sai Su”: Mai Ciki Ta Kona Miyan Abincinta, Ta Sharbi Abun ta Hoto: @berry_china
Asali: TikTok

A cewarta, ta tashi kona miyan ne da misalin karfe 2:00 na tsakar dare saboda wannan ne abun da jinjirin cikinta ke bukata.

"Sai da na tashi da misalin 2:00 na tsakar dare don dumama miyan har sai da ya kone kafin na iya shan sa saboda wannan ne abun da dan cikina ke so. Kwadayin ciki babu yadda mutum ya iya", cewarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama'a sun yi martani

@loveth339ta ce:

"Kowa na magana kan kwadayin nan. Amma ni ban taba jin kwadayi ba tun da na dauki ciki faaaaa."

@sym_bee ta yi martani:

"Nawa indomie ne da karin yaji da ruwa."

@mamap_17 ta yi martani:

"Ni ban yi kwadayin komai ba da nake da ciki."

@debb1034 ta ce:

"Nawa farfesu ne mai tsananin yaji."

@bate218 ta ce:

"Ina ga ni da nake kwadayin gawayi."

Kara karanta wannan

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

@user125727599943 ya ce:

"Nawa teba ne da miyan kubewa."

@robinhood983 ta ce:

"Ki daina! Ki yi ki haihu mu huta."

Kalli bidiyon a kasa:

Samun kwanciyar aure mai kyau ne sirrin tsawon raina, yar shekaru 102

A wani labari na daban, wata tsohuwa da ta yi bikin cika shekaru 102 a duniya ta bayyana sirrin da ke tattare da tsawon ranta.

Matar mai suna Joyce Jackman ta bayyana cewa samun namijin wanda ya iya kwanciyar aure da kyau shine babban dalilin da yasa ta yi tsawon rai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel