“Zan Yi Kewar Zagaye Fadar Shugaban Kasa Da Na Kan Yi Da Yamma”, Aisha Buhari
- Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta magantu kan abun da za ta yi kewa game da fadar shugaban kasa wacce suka shafe shekaru takwas a cikinta
- Aisha Buhari ta ce za ta yi kewar yadda ta kan fita ta ja kafa a lambun fadar shugaban kasa duk yammaci
- A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne iyalan shugaban kasar za su bar gidan gwamnati domin iyalan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu su samu matsuguni a ciki
Matar shugaban kasa mai barin gado, Aisha Buhari, ta bayyana abun da za ta yi kewa game da fadar shugaban kasa.
Mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shekaru takwas wanda ya fara a ranar 29 ga watan Mayun 2015 zai zo karshe a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Zan yi kewar jan kafa da na kan yi da yamma a fadar shugaban kasa, Aisha Buhari
A wata hira ta musamman da jaridar The Sun, Aisha ta ce za ta yi kewar zagayawa fadar shugaban kasa da yammaci, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aisha ta ce:
"Bayan shekaru takwas a villa, na kan ce zan yi kewar jan kafa da yamma. Kun sani, suna dogon lambu mai dan karan kyau, ina ganin zan yi kewar wannan. Baya ga haka, za mu bar gidan cike da farin ciki. Kuma mun godewa Allah."
A ranar Alhamis, ne Aisha Buhari ta mika ragamar shugabanci ga matar shugaban kasa mai jiran gado, Oluremi Tinubu.
An yi bikin mika mulkin ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja inda Aisha ta mikawa Remi wasu muhimman takardu na ofishin matar shugaban kasa.
Matan shugaban kasa sun cancanci a musu alfarma, Aisha Buhari
A baya mun ji cewa, uwargidar shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta ce matan tsoffin shugabanni sun cancanci a masu alfarma ta musamman kamar yadda ake yi wa mazajensu.
A cewar matar shugaban kasar, ya kamata a dunga ba matan shugaban kasa ababen hawa, kula da lafiyarsu da basu alawus kamar yadda ake yi wa tsoffin shugabannin kasa.
Aisha ta fadi hakan ne a wajen kaddamar da wata takarda a Abuja wanda shugabar kungiyar matan tsaro da na yan sanda (DEPOWA), Misis Vickie Anwuli Irabor ta wallafa.
Asali: Legit.ng