Gwamna Wike Ya Bukaci FG Ta Kara Yawan Kasafin da Take Ware Wa Yan Sanda

Gwamna Wike Ya Bukaci FG Ta Kara Yawan Kasafin da Take Ware Wa Yan Sanda

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya roki gwamnatin tarayya ta kara yawan kasafin hukumar yan sanda
  • Gwamnan da ke gab da sauka daga mulki, ya ce hakan zai bai wa yan sanda damar gudanar da ayyukan da ke kansu cikin daɗin rai
  • Ya faɗi haka ne a wurin kaddamar cibiyar 'yan sanda da gwamnatinsa ta gina a Rumuepirikom, karamar hukumar Obio/Akpor

Rivers - Gwamna mai barin gado a jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jaddada cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta ƙara yawan kudaɗen da take ware wa rundunar 'yan sanda.

Gwamna Wike, mamban jam'iyyar PDP ya bayyana cewa hakan zai bai wa hukumar yan sanda damar sauke nauyin da ke kanta fiye da yadda ake tsammani.

Wike.
Gwamna Wike Ya Bukaci FG Ta Kara Yawan Kasafin da Take Ware Wa Yan Sanda Hoto: SSG Rivers State Government
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren gwamnatin Ribas ya wallafa a Facebook ɗauke da sa hannun mai bai wa gwamna shawara ta musamman kan midiya, Kelvin Ebiri.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Kori Kwamishinoni da Hadimai, Ya Kafa Musu Sharaɗi

Ya ce duk gwamnatin da ba zata iya kare rayuka da kadarorin al'ummarta ba, ba zata yaƙi aikata muggan laifuka ba kuma ta gaza sanya mutane farin ciki, to jahila ce a fannin shugabanci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wike ya yi wannan furucin ne a garin Rumuepirikom yayin kaddamar da cibiyar fasaha ta hukumar yan sanda a karamar hukumar Obio/Akpor.

A cewarsa, gwamnatinsa ta fahimcin tasirin samar da kayan aiki shiyasa take duk mai yuwuwa wajen samar da kayan aiki ga rundunar 'yan sanda reshen jihar Ribas.

Ya ce irin waɗannan taimakon suna taka rawa wajen inganta ayyukan jami'an yan sanda, su yi bakin kokarinsu wajen dakile yawaitar ayyukan laifi a jihar Ribas.

A kalamansa kamar yadda Sanarwan ta bayyana, Wike ya ce:

"Namu shi ne mu samar da muhimman kayan aiki kana mu bar wuka da nama hannun 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da nasu aikin.

Kara karanta wannan

Gwamna Arewa Ya Kori Kwamishinoni da Hadimansa Daga Aiki, Ya Ba Su Umarni Nan Take

"Idan har aka samu wadataccen mahalli mai kyau, jami'an hukumomin tsaro zasu yi bakin gwarwado. Kamar yadda CP ya faɗa, da zaran tawagar dabaru sun dawo nan, wurin kaɗai zai basu damar zage dantse su yi aiki."

Gwamnan Ogun ya rushe majalisar zartarwa

A wani labarin kuma Gwamna Abiodun ya sallami mambobin majalisar zartarwa, Ya musu kyautar rabuwa mai tsoka.

Dapo Abiodun na jihar Ogun ya sallami kwamishinoni da sauran hadimansa gabanin ranar rantsarwa kuma ya shirya musu kyautar rabuwa mai tsoka da za'a baiwa kowanensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262