Cikakken Jerin Ranakun Hutu Da Yan Najeriya Za Su Mora A Shekarar 2023
A bukukuwan sabuwar shekara da ake yi, ranar Lahadi 1 ga watan Janairu, ‘yan Najeriya za su huta kuma ba za su je aiki ba a ranar Litinin 2 ga watan Janairu saboda bin ka’idar da gwamnatin tarayya ta bayar na hutun aiki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Ranar hutun sabuwar shekara na daya daga cikin hutu 16 da ‘yan Najeriya za su mora a wannan shekara ta 2023.
A duk lokacin sa gwamnatin tarayya ta sanar da ranar hutu daga ma’aikatar cikin gida, hakan na nufin makaranti da kasuwanni da bankuna da kuma ofisoshin gwamnati za su kasance a kulle a wannan ranar.
Ganin cewa hutu yana taimaka wa mutane wajen tsara jadawalin rayuwarsu, Legit.ng ta tattaro muku ranakun hutu a Najeriya da gwamnati ta bayar na shekarar 2023.
Ga jerin ranakun hutu a Najeriya na shekarar 2023.
1. Lahadi, 1 ga watan Janairu – hutun sabuwar shekara
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Litinin, 2 ga watan Janairu – hutun sabuwar shekara (saboda ranar hutun ta kasance a ranar Lahadi)
3. Juma’a, 7 ga watan Afrilu – hutun ranar ‘Good Friday’
4. Litinin, 10 ga watan Afrilu – hutun ranar ‘Easter Monday’
5. Asabar, 22 ga watan Afrilu – hutun sallah karama
6. Lahadi, 23 ga watan Afrilu – hutun sallah karama
7. Litinin, 1 ga watan Mayu – hutun ranar ma’aikata
8. Asabar, 27 ga watan Mayu – hutun ranar yara (makarantu da dalibai kadai)
9. Litinin, 12 ga watan Yuni – hutun ranar dimukradiyya
10. Alhamis, 29 ga watan Yuni – hutun babbar sallah
11. Juma’a, 30 ga watan Yuni – hutun babbar sallah
12. Laraba, 27 ga watan Satumba – hutun ranar Maulidi
13. Lahadi, 1 ga watan Oktoba – hutun ranar ‘yancin kasa
14. Litinin, 2 ga watan Oktoba – hutun ranar ‘yanci (saboda ranar hutun ta kasance ranar Lahadi)
15. Litinin, 25 ga watan Disamba – hutun ranar Kirsimeti
16. Talata, 26 ga watan Disamba – hutun ranar Dambe
Jerin Sunayen Manyan ’Yan Siyasar Najeriya da Suka Mallaki Jami’o’i Masu Zaman Kansu
A wani labarin, a Najeriya jami'o'in gwamnati suna fama da matsaloli daban-daban da suka hada da yajin aikin malaman jami'o'i da rashin ingantattun dakunan karatu da gwaji.
Legit.ng ta tattaro cewa Najeriya na da jami'o'i masu zaman kansu fiye da 100 wadanda gwamnati ta amince da su.
Daga cikin 'yan siyasan da suka mallaki jami'o'in akwai Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo da Rochas Okorocha da kuma Datti Baba-Ahmed da sauransu.
Asali: Legit.ng