Farashin Tumatur Ya Fadi Warwas a Najeriya Sakamakon Shigo Da Shi Daga Wasu Kasashen Nahiyar Afirka

Farashin Tumatur Ya Fadi Warwas a Najeriya Sakamakon Shigo Da Shi Daga Wasu Kasashen Nahiyar Afirka

  • An samu faduwar farashin tumatur a kasuwanni da dama a Najeriya saboda shigo da shi daga wasu kasashe
  • An samu karancin tumatur a kwanakin baya sakamakon matsalar kwari da suka lalata gonakin tumatur
  • A baya ana siyan babban buhun tumatur N50,000 amma yanzu farashin ya fado zuwa N18,000 ko N20,000

Jihar Kano - Farashin kayan gwari musamman tumatur ya fadi a mafi yawan kasuwannin Najeriya sakamakon karin shigowa da shi daga kasashen Ghana da Cameroon.

Bincike ya bayyana yadda a baya aka samu karancin tumatur din a mafi yawan kasuwannin kasar sakamakon lalata shi da kwari su ka yi a mafi yawan gonakin tumatur a kasar.

Tumatur a Kasuwannin Najeriya
Farashin Tumatur Ya Fadi Warwas a Najeriya. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa dilolin tumatur din sun yanke shawarar shigo da shi daga kasashen Ghana da Cameroon saboda maye gurbin wadanda aka rasa don yalwata shi a kasar.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba Za Mu Daina Bada Kwangiloli da Cin Bashi ba Sai Daren 29 ga Watan Mayu

Dalilin faduwar farashin tumatur a kasar

Wadannan a cewar rahotanni na daya daga cikin dalilan da suka sa tumatur din farashin shi ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da kwanakin baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Binciken ya tabbatar da cewa baban buhun tumatur da a baya ake siyar da shi akan kudi N50,000, a yanzu ya sauko zuwa N18,000 zuwa N20,000 a jihar Kano saboda yawansa a kasuwanni.

Shugaban kungiyar masu noman tumatur ya magantu

Shugaban kungiyar masu noman tumatur (TOGAN) a jihar Kano, Alhaji Sani Danladi Yadakwari ya bayyana cewa karancin tumatur da aka samu a baya bai rasa nasaba da kwari da suka lalata gonaki da yawa, yayin da ya ce shigo da tumatur din daga kasashe biyu a Nahiyar Afirka da kuma jihar Ogun daga Najeriya ya taimaka kwarai wurin faduwar farashin tumatur din a kasar.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Gwamna Ya Nemi Alfarmar Karshe Kafin Buhari Ya Bar Fadar Aso Rock

A cewarsa:

“Mun shigo da karin tumatur daga jihar Ogun ta Najeriya, sannan da kuma kasashen Nahiyar Afirka guda biyu, Ghana da Cameroon, dilolin tumatur sun yi nasarar karya farashin tumatur din kuma yanzu ya yi yawa a kasuwanni yadda aka so.”

Farashin kayan abinci sun fadi war-was a Kano ana daf da fara azumin Ramadan

A wani labarin, rahotanni sun tabbatar da cewa wasu daga cikin kayan abinci sun fadi warwas a wasu kasuwanni a jihar Kano.

An bayyana cewa farashin kayan miya da ganye sun fadi da 200% a wasu kasuwanni a Kofar Wambai da Rimi duk a cikin jihar Kano.

Faduwar farashin kayan na zuwa ne ana daf da fara azumin watan Ramadan a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.