Jerin Yaruka 17 mafi shahara a fadin duniya
A wani sabon bincike da aka gudanar ya bayyana cewa, yaren hausa shine yaren da yafi shahara a yankin Arewacin Najeriya da wasu sassa na kasashen Afirka. Binciken ya tabbatar da cewa, yaren hausa shine yare na 11 mafi shahara a fadin duniya.
A kididdigar da Spectator Index ta fitar, akwai kimanin mutane miliyan 150 dake magana da harshen Hausa a fadin duniya baki daya, inda kimanin mutane miliyan 2 ke amfani da yaren Punjabi na kasar Indiya da kuma kimanin miliyan 21 dake amfani da yaren Jamus.
Yaren Mandarin na kasar Sin shine yare mafi shahara a ilahirin duniya baki daya, inda kimanin mutane biliyan 1.09 ke amfani da shi. Sai kuma yaren Turanci mai take masa baya a shahara da kimamin mutane miliyan 983.
Legit.ng da sanadin shafin www.nairaland.com ta kawo muku jerin yaruka 17 mafi shahara a fadin duniya tare da adadin mutane dake amfani da su kamar haka:
1. Mandarin: 1090m
2. Turanci: 983m
3. Hindustani: 544m
4. Spanish: 527m
5. Larabci: 422m
6. Malay: 281m
7. Russia: 267m
8. Bengali: 261m
KARANTA KUMA: Jerin sunayen manyan Kabilu da jihohin su a Najeriya
9. Portuguese: 229m
10. Faransanci: 229m
11. Hausa: 150m
12. Punjabi: 148m
13. Jamusanci: 129m
14. Japanese: 129m
15. Persian: 121m
16. Swahili: 107m
17. Telugu: 92m
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng