Farashin wasu kayan abinci sun fadi war-was a Kano ana daf da fara azumin Ramadan

Farashin wasu kayan abinci sun fadi war-was a Kano ana daf da fara azumin Ramadan

- Rahotanni sun nuna cewa kayan gwari sun yi araha a kasuwannin Kano

- Har zuwa yanzu ba a gama shigo da kayan miya da ganye daga gonaki ba

- Kayan sun cika kasuwanni ne saboda manoma sun samu amfani da rani

Rahotanni daga hukumar dillancin labarai na kasa watau NAN su na zuwa cewa farashin kayan gwari da ganye sun yi kasa a kasuwannin jihar Kano.

Darajar kayan miya da ganye da sauran makusanta kasa ya fadi yanzu da sama da 200% a kasuwannin Kofar Wambai da na Rimi a cikin garin Kano.

Tumaturi, tattasai, tarugu, da albasa sun dawo sun yi araha bayan tsadar da su ka yi kwanakin baya.

NAN ta ce an samu saukin farashi ne a sakamakon yawan da kayan gwarin su ka yi a gonaki, ana ta fito da sababbin amfanin gonaki da lambuna har gobe.

KU KARANTA: Fetur ya zama gwal, gidajen mai sun rufe, wasu na saidawa da tsada

Kashin albasar da ake saida wa N250 ya dawo N100 a yau, tumatiri da tarugun da aka saba saye a kan N400 da N600 sun koma N100 da N150 a kasuwanni.

Wani ‘dan kasuwa, Malam Ibrahim Danborno, ya ce kayan sun yi yawa a gonaki don haka farashi ya ki tashi, ya ce har yanzu ana fito da kaya daga gona.

Sabiu Ismaila yake cewa kayan ganye da na miya sun cika kasuwa ne saboda an yi dacen noman rani.

Abubakar Danladi, wanda yake saida tumaturi, ya ce dole farashi ya sauka saboda gudun mutane su yi asarar amfanin gonansu, tun da ba a iya adana kayan miya.

KU KARANTA: Matasa 460, 000 sun samu kyautar N500, 000 na tallafin Coronavirus

Farashin wasu kayan abinci sun fadi war-was a Kano ana daf da fara azumin Ramadan
Kayan gwari Hoto: www.independent.ng
Asali: UGC

A lokacin da wata daya ya rage a fara azumi, wasu su na fatan farashin hatsi su yi kasa kamar yadda ganye da kayan miya su ka fadi war-was a halin yanzu.

A watan nan aka ji cewa dillalan shanu da na kayan abinci sun shiga yajin aikin kai kaya zuwa kasar kudu biyo bayan kin sauraranta da gwamnatin tarayya ta yi.

Hakan na zuwa ne bayan kisa da barnar da aka yi wa mutanen Arewa da ke zaune a jihar Oyo.

Daga baya 'yan kasuwan sun janye yajin-aikin, aka cigaba da shiga da abinci zuwa Kudancin kasar, amma kafin nan an yi ta kukan karancin abinci a yankin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng