Nnamdi Kanu: Gwamna Ya Nemi Alfarmar Karshe Kafin Buhari Ya Bar Fadar Aso Rock
- Mai girma Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya sake rokon gwamnati ta fito da Nnamdi Kanu
- Gwaman Anambra ya na so a saki Shugaban kungiyar IPOB kafin Muhammadu Buhari ya sauka
- Soludo ya bukaci Shugaban kasa ya bi shawarar majalisar dinkin Duniya da hukuncin kotu
Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo ya roki Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saki Nnamdi Kanu.
Premium Times ta ce Gwamna Charles Chukwuma Soludo ya nemi a fito da Nnamdi Kanu kafin wa’adin Muhammadu Buhari ya cika a ranar Litinin.
A ranar 20 ga watan Afrilu ne Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya yi wannan kira a wata wasika ta musamman da ya aika zuwa fadar shugaban kasa.
Gwamnan na Anambra ya nuna cewa cigaba da tsare Mazi Kanu da gwamnatin tarayya ta ke yi ya na da mummunan tasiri ga mazauna yankinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ana hana mutane fita
A dalilin garkame shugaban na kungiyar IPOB, jama’a ba su iya fita daga gidajensu a ranakun Litinin saboda tsaron abin da zai iya biyo baya a yankin.
Farfesa Soludo ya yi mamakin yadda gwamnatin tarayya ta yi kunnen kashi duk da majalisar dinkin Duniya ta bada shawarar a fito da Kani tun tuni.
"A dalilin cigaba da rufe Mazi Kanu, a yanzu an kirkiro abin da za a iya kira da matsalar rashin tsaro da gan-gan da Kudu maso gabas.
Wasu daga cikin magoya bayan Mazi Kanu sun kakaba dokar hana fita daga gidaje a duk Litinin a Kudu maso gabas, sannan ana ta’adi...
...miyagu, masu garkuwa, ‘yan bindiga zuwa ‘yan fanshi da sauransu su na barna da sunan masu karbar ‘yanci ko fafutukar fito da Kanu.
- Charles C. Soludo
Kanu bai da lafiya
Jaridar ta ce wasikar ta kuma tunawa shugaban mai barin gado irin halin da Kanu ya ke ciki na rashin lafiya, yake cewa DSS ba ta iya kula da shi ba.
A shirye Soludo ya ke da ya karbi belin Kanu, ya na rokon ayi wa majalisar dinkin Duniya da kotun tarayya biyayya, ya ce hakan ne abin da ya dace.
Shari'a Ambrose Owuru
A wata shari'a da aka zartar a ranar Alhamis, an ji labari Kotu ta ce wani mai neman hana rantsar da Bola Tinubu da Kashim Shettima ya biya N40m.
Ambrose Owuru zai biya miliyoyi ga Muhammadu Buhari, AGF, Bola Tinubu da INEC saboda batawa kotu lokaci da ya yi na dawo da tsohuwar shari'a.
Asali: Legit.ng