Alkalai Sun Laftawa ‘Dan Takara Ukubar N40m da Ya Nemi Ya Hana Rantsar da Tinubu

Alkalai Sun Laftawa ‘Dan Takara Ukubar N40m da Ya Nemi Ya Hana Rantsar da Tinubu

  • Ambrose Owuru ya dumfari kotu da nufin hana Bola Tinubu shiga ofis a matsayin shugaban kasa
  • A hukuncin da aka zartar a yau, Alkalai sun ladabtar da tsohon ‘dan takaran shugaban Najeriya
  • Owuru bai yi nasara ba, kotun daukaka kara ta ce dole ya biya N40m ga wadanda ya yi kara a gabanta

Abuja - The Nation ta ce Kotun daukaka kara ta saurari karar Ambrose Owuru, a karshe ta yankewa tsohon ‘dan takaran shugaban kasar hukunci.

Babban kotun mai zama a garin Abuja ta ce Ambrose Owuru zai biya N40m a dalilin shigar da kararsa ya na neman a ki rantsar da Bola Ahmed Tinubu.

Kotun ta bukaci wanda ya shigar da karar ya biya N10m ga Muhammadu Buhari da wani N10m ga babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami SAN.

Kara karanta wannan

Kafin Buhari Ya Sauka Daga Mulki, An Samu Wanda Ya Maka Shugaban Kasa a Kotu

Tinubu
Bola Tinubu ya samu lambar GFCR Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

Haka zalika Owuru zai biya N10m ga kowane daga cikin hukumar zabe ta INEC da Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin Jamil Tukur

Rahoton ya ce Mai shari’a Jamil Tukur ya karanto wannan hukunci da shi da sauran Alkalai biyu su ka zartar bayan sun kammala sauraron shari’ar.

Tukur ya zargi wanda ya yi kara da batawa kotu lokaci da neman fusata shugaban kasa, Ministan shari’a, hukumar zabe da Tinubu da aka yi kararsu.

Alkalin ya soki Owuru a kan kokarinsa na dawo da maganar da aka birne tun a 2019 a kotun koli.

Mai shari’an ya ce babu dalilin maido zancen da an yi fatali da shi saboda rashin hujjoji, ya zargi Owuru da niyyar hada su fada da kotun Allah ya isa.

A watan Afrilun nan tsohon ‘dan takaran shugaban kasar ya je kotu ya na kalubalantar zaben Najeriya da aka yi shekaru hudu da suka wuce.

Kara karanta wannan

An Daure Lakcara Shekaru 5 a Gidan Kaso Bisa Zargin Sama da Fadi da N6m Na Tallafin Karatunsa

The Cable ta ce ‘dan siyasar ya shigar da kara mai lamba CA/CV/259/2023, ya na mai rokon a hana Muhammadu Buhari ya mika mulki ga Bola Tinubu.

Lauyoyinsa sun yi ikirarin shi ne ainihin zababben shugaban kasa a 2019 kuma bai shiga ofis ba.

Dabarar Tinubu a 2023

An rahoto 'dan takarar Gwamnan Oyo a LP a zaben 2023, Tawfiq Akinwale ya ce Peter Obi yaron Bola Tinubu ne, da shi aka yi amfani saboda APC ta ci zabe.

Akinwale ya ce sai da ta kai Tinubu ya tallafawa jam'iyyar LP da kudi domin Obi ya karya Atiku Abubakar bayan an roki Pat Utomi ya janye masa takara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel