“Abun a Jini Yake”: Bidiyon Matashiya Da Ke Hakora Irin Na Mahaifiyarta Ya Dauka Hankali

“Abun a Jini Yake”: Bidiyon Matashiya Da Ke Hakora Irin Na Mahaifiyarta Ya Dauka Hankali

  • Tsananin kama tsakanin wata matashiya da mahaifiyarta ya baiwa mutane da dama mamaki kuma ya sanya su tofa albarkacin bakunansu a TikTok
  • A bidiyon da @motherj24 ta wallafa, matashiyar ta nuna mahaifiyarta wacce ke da hakora sak irin nata
  • Nan take bidiyon ya dauka hankalin masu amfani da TikTok wadanda tsananin kaman da uwa da 'yar ke yi ya basu mamaki

Wata matashiyar budurwa ta wallafa wani bidiyo a TikTok don nunawa mutane tsananin kaman da ke tsakaninta da mahaifiyarta.

Shafin @motherj24 ne ya wallafa bidiyon, kuma ya nuna cewa diyar da mahaifiyarta suna da jerin hakora iri guda.

Uwa da yarta masu kama
“Abun a Jini Yake”: Bidiyon Matashiya Da Ke Hakora Irin Na Mahaifiyarta Ya Dauka Hankali Hoto: TikTok/@motherj24.
Asali: TikTok

A bidiyion mai tsawon sakan 29, an gano matashiyar tana kiran mahaifiyarta kan ta fito gaban kamara sannan ta nuna kanta.

Uwa da ya masu jerin hakora iri daya a bidiyo da ya yadu

Kara karanta wannan

“Yan Matan Nan Sun Cancanci Taimako”: Kyawawan Yan Mata Da Ke Aiki a Kamfanin Yin Biskit Sun Burge Jama’a

Sai dai kafin mahaifiyarta ta bayyana, jerin hakorar matashiyar ya rigada ya dauki hankalin mabiyanta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutane sun zama cikin shiri, suna son ganin yaya kamannin mahaifiyarta yake. Lokacin da ta bayyana, bata ba masu kallo kunya ba.

Hakoran mahaifiyar tata ya yi kama da nata sosai, inda ya zazzago daga cikin bakin zuwa labbanta na kasa.

Mutane sun cika da mamaki lokacin da suka ga hakoran matar da yadda ya yi kama da na diyarta.

Nan take masu amfani da TikTok suka garzaya sashin sharhi domin nuna sha'awarsu ga uwa da diyar tata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@bolajiadesoye4 ya ce:

"Lallai ita din yar mahaifiyarta ce."

@Bouna85 ta yi martani:

"Abun na dangi ne."

@passye beauty salon ta ce:

"Me ke faruwa a nan?"

@Cyndilecoeur025 ta yi martani:

Kara karanta wannan

Ai Ko Da Sake: Bidiyon Sauyin Da Wata Tsohuwa Ta Samu Bayan Ta Sha Kwalliya Ya Bar Baya Da Kura

"Abun da ya fi muhimmanci shine cewa ke da mahaifiyarki kuna farin ciki."

@cool Kalemba ta ce:

"Ina mamakin dalilin da yake sawa muna caccakar kuskuren wasu alhalin mun san cewa ba yinsu bane?? Yan uwana maza da mata Allah ya yafe maku."

Matashiya ta koka bayan bunsuru ya rufko cikin dakinta ta saman sili

A wani labari na daban, wata matashiya ta koka bayan wani bunsuru ya rufto cikin dakinta ta sili tana tsaka da sharar bacci.

Matashiyar ta ce babban abun da ya fi bata tsoro da mamaki shine ta yadda aka yi bunsurun ya hau sama har ya kai ga silinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel