Kaman Almara: Matashiya Ta Wallafa Hotunan Wani Bunsuru Da Ya Fado Dakinta Ta Silin Tana Tsaka Da Bacci

Kaman Almara: Matashiya Ta Wallafa Hotunan Wani Bunsuru Da Ya Fado Dakinta Ta Silin Tana Tsaka Da Bacci

  • Wata matashiya yar Najeriya ta bayyana arangamarta da wani bunsuru da ya shiga gidanta da sanyin safiya
  • A cewar matashiyar, ita da ahlinta suna tsaka da bacci ne lokacin da bunsurun ya fado daga saman sili
  • A wallafarta, ta koka cewa bata da masaniya daga inda bunsurun ya fito ko abun da ya sa ya fado cikin gidanta

Wata matashiya yar Najeriya ta wallafa hotuna a Twitter bayan wani bunsuru ya shigar mata gida.

A cewar matashiyar mai suna @oluwateepsy2 a Twitter, tana tsaka da bacci tare da ahlinta ne lokacin da suka ji karan faduwar abu.

Akuya, fasasshen sili da karyayyen fanka
Kaman Almara: Matashiya Ta Wallafa Hotunan Wani Bunsuru Da Ya Fado Dakinta Ta Silin Tana Tsaka Da Bacci Hoto: @oluwateepsy2/Twitter
Asali: Twitter

Gaba dayansu suka tashi sai kawai suka yi ido hudu da bunsuru a kasa. Ya fado ne daga saman sili sannan ya bata masu fankarsu ta tsaye.

Da take wallafa hotunan bayan afkuwar komai, ta koka cewa abun mamaki ne da ban al'ajabi saboda bata san daga ina bunsurun ya fito ba kuma bata san mamallakinsa ba.

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Kalamai Masu Ratsa Zuciya A Taron Bankwana

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalamanta:

"Da misalin karfe 7 na safiyar nan, ni da mutanena muna bacci lokacin da kwatsam muka ga wani bunsuru yana fadowa daga saman silinmu. Abun akwai ban tsoro da dariya a lokaci guda saboda mun kasa gane abun ma. Ya bata mana fanka ma.
"Daga inda bunsurun ya fito, ba mu sani ba. Wa ke da bunsurun, ba mu sani ba. Ta yaya ya isa ga saman sili? Allah kadai ya sani. Abun da ya yi saura shine siyar da shi don gyara sili da siyan sabuwar fanka. Ko me kuke tunani?"

Jama'a sun yi martani

Fumnanya ta ce:

"Shin Annabi Ibrahim ya yi wa Allah tambayoyi a lokacin da ya gabatar masa da rago? A'a. Toh me yasa kike yi kamar baki yarda da Allah ba."

Cryptic preacher ya ce:

Kara karanta wannan

A Majami'a Nake Kwana: Wani Ya Roki Kotu Ta Raba Aurensu Saboda Barazanar Kisa da Matarsa Ke Masa

"Ki siyar da shi, ya yi tsada yanzu, za ki samu akalla 60k kan sa, zai ishe ki gyara silin da siyan sabuwar fanka."

TyOlajide ta ce:

"Haha, lallai wannan tashin ba zata ne! Ina ganin kina iya cewa silin dinki ya zama G.O.A.T a hukumace."

Ya fi babu: matashiya ta gwangaje kanta da dan karamin gida

A wani labarin kuma, wata matashiya ta tattara yan kudaden da take da su inda ta ginawa kanta dan karamin gida don huce takaicin biyan kudin haya.

Matashiyar ta ce duk da kankantar gidan, tana matukar alfahari da shi don ta mallaki abun da za ta kira da nata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel