29 Ga Mayu: DSS Ta Bankado Shirin Da Wasu Ke Yi Na Tarwatsa Bikin Rantsar Da Shugaban Kasa Da Gwamnoni

29 Ga Mayu: DSS Ta Bankado Shirin Da Wasu Ke Yi Na Tarwatsa Bikin Rantsar Da Shugaban Kasa Da Gwamnoni

  • Hukumar DSS ta ce ta gano kulla-kullan da wasu bata gari ke yi don tarwatsa bikin rantsarwa na ranar 29 ga watan Mayu
  • Rundunar tsaron ta yi gargadin cewa ba za ta bari irin wadannan mutane marasa kishin kasa su kawo tsaiko wajen mika mulki a kowani yanki na kasar ba
  • A cewar DSS manufar wadannan mutane shine kawo karan tsaye ga kokarin hukumomin tsaro na ganin an yi bikin cikin lumana

Abuja - Rundunar tsaro ba farin kaya wato DSS ta ce tana sane da shirye-shiryen da wasu bata gari ke yi na tarwatsa bikin rantar da shugaban kasa da gwamnoni a ranar 29 ga watan Mayu a fadin kasar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Dr Peter Afunanya, ya saki a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

An Daure Lakcara Shekaru 5 a Gidan Kaso Bisa Zargin Sama da Fadi da N6m Na Tallafin Karatunsa

Afunanya ya ce manufar ita ce kawo karan tsaye ga kokarin hukumomin tsaro wajen tabbatar da gudanar da bikin cikin zaman lafiya da haifar da tsoro da fargaba tsakanin al'umma, jaridar The Nation ta rahoto.

Jami'an rundunar tsaro ta farin kaya
29 Ga Mayu: DSS Ta Bankado Shirin Da Wasu Ke Yi Na Tarwatsa Bikin Rantsar Da Shugaban Kasa Da Gwamnoni Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Rundunar ta shawarci yan Najeriya da su bi ka'idojin tsaro da aka gindaya da kyau yayin gudanar da bikin rantsarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DSS ta gargadi yan Najeriya gabannin 29 ga watan Mayu

Kakakin rundunar ya kara da cewar ana gargadin wadanda ba a ba izini ba da su nisanci wuraren da aka kebe da wasu wurare na musamman a wajen taron, rahoton Punch.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Idan za a iya tunawa a ranar 18 ga watan Mayun 2023, babban sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin mika mulki na shugaban kasa (PTC) ya gudanar da taron manema labarai na duniya inda ya bayyana tsare-tsaren rantsar da shugaban kasa.

Kara karanta wannan

29 Ga Watan Mayu: Gwamnan PDP Ya Yi Sabbin Nade-Nade Gabannin Barinsa Kujerar Mulki

"Babban abun jan hankali cikin tsare-tsaren shine rantsar da shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a Abuja. A wannan rana ne za a kuma rantsar da sabbin gwamnoni a yawancin jihohin.
"Saboda haka, rundunar na sane da shirye-shiryen da wasu bata gari ke yi na tarwatsa shirin a yankunan kasar. Manufar shine dakile kokarin hukumomin tsaro na tabbatar da anyi bukukuwan cikin zaman lafiya da kuma haifar da fargaba da tsoro a tsakanin jama'a.
"Bisa ga haka, ana shawartan yan kasa, kafofin watsa labarai da kungiyoyin jama'a da su bi ka'idoji tsaro yayin bukukuwan. Ana kuma umurtansu da su guje ma labaran karya, kokawar karya, karkatattun rahoto da labarai wanda ka iya rura wutar rabuwar kai, tayar da hankali da kuma barkewar rikici kafin da bayan taron. Hakan ya kasance ne daboda irin wannan ayyuka babu abun da zai amfani jama'a face lalata hadin kan kasar ."

Kara karanta wannan

Ban Damu da Rantsar da Tinubu Ba, Kotu Za Ta Iya Karban Mulki Ko da an Rantsar da Shi – Atiku

A halin da ake ciki, rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da kwantar da hankalinsu sannan su bi doka inda ta ce za ta ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da an yi bikin rantsarwar cikin nasara.

Ganduje ya mika rahoton mika mulki ga Abba Gida-Gida

A wani labarin, gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ta gabatar da rahoton mika mulki ga zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Ganduje ya bukaci kwamitin na NNPP da ya yi nazari a kan rahoton sannan ya gabatar da jawabinsa gabannin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng