Da Dumi-Dumi: Mahajjatan Najeriya Sun Yi Hatsarin Mota A Hanyar Zuwa Abuja

Da Dumi-Dumi: Mahajjatan Najeriya Sun Yi Hatsarin Mota A Hanyar Zuwa Abuja

  • Wata motar bas dauke da maniyyata 'yan jihar Nasarawa ta yi hatsarin akan hanyarsu na zuwa Abuja
  • Motar bas din mai dauke da wurin zama 18 ta yi hatsarin ne a Kara cikin karamar hukumar Keffi
  • Hukumar Alhazai ta kasa za ta fara jigilar maniyyata a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu da jihar Nasarawa

FCT, Abuja – Wata motar bas dauke da mahajjata daga jihar Nasarawa zuwa Abuja don tafiya kasa mai tsarki ta yi hatsari.

Daily Trust ta tattaro cewa motar bas din mai dauke da wurin zama 18 ta yi hatsarin ne a kusa da Kara a karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa a ranar Laraba 24 ga watan Mayu.

Mahahajjata sun yi hatsarin mota a hanyar zuwa Abuja
Mahajjata Sun Yi Hatsari Akan Hanyarsu Ta Abuja Daga Jihar Nasarawa Don Tafiya Kasa Mai Tsarki. Hoto: The News Guru
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Karin Bayani: CBN Ya Kara Kudin Ruwa Zuwa Kashi 18 'Don Dakile Hauhawan Farashin Kaya'

Har yanzu ana kan tattara bayanai akan musabbabin hatsarin motar, yayin da aka tabbatar da cewa mutane da dama sun samu raunuka.

Za a fara jigilar Alhazai da jihar Nasarawa

Rahotanni sun tattaro cewa Hukumar Alhazai ta kasa ta shirya tsab don fara jigilar Alhazai da jihar Nasarawa na wannan shekara ta 2023 a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu, kafin wannan iftila'i ya afku.

Hukumar Alhazai ta magantu akan abin da ya faru

Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Musa ya jajantawa wadanda abin ya shafa da iyalansu, yayin da ya tabbatar cewa hukumar za ta yi duk abin da ya dace don samar da walwala.

Har ila yau. Hukumar Alhazai ta kasa ta nuna alhininta da kuma goyon baya ga maniyyatan da kuma jihar ta Nasarawa, cewar rahotanni.

Hukumar ta kara da cewa za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin da suka dace don samar da kyakkyawan kulawa da kuma horo ga maniyyata.

Kara karanta wannan

An Daure Lakcara Shekaru 5 a Gidan Kaso Bisa Zargin Sama da Fadi da N6m Na Tallafin Karatunsa

NAHCON Ta Sauya Magana Kan Ƙarin Kuɗin Kujerar Hajjin Bana 2023

A wani labarin, Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta janye maganar da ta yi na cewa maniyyata ba za su biya ko sisin kwabo ba daga karin da aka samu akan kowace kujera ta Hajjin bana.

Rahotanni sun tattaro cewa kamfanonin jiragen sama masu jigilar maniyyata zuwa kasar mai tsarki ta Saudiyya sun bukaci maniyyatan su kara $250 akan kowace kujera, saboda rikicin kasar Sudan da ake fama da shi a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel