Saura Kwana 6: Na Matsu Na Gama Mulkina Saboda Matsin Lamba, Buhari Ya Koka Kan Yawan Tarurruka

Saura Kwana 6: Na Matsu Na Gama Mulkina Saboda Matsin Lamba, Buhari Ya Koka Kan Yawan Tarurruka

  • Shugaba Buhari ya bayyana yadda ya matsu kwanaki shida su kare na mulkinsa don matsin lamba da yake samu
  • Buhari ya fadi haka ne a taron cin abinci don karrama shi a ranar Talata 23 ga watan Mayu a babban birnin kasar, Abuja
  • Ya kara da cewa cikin kwanakin nan yana da jerin tarurruka da kuma abubuwan da zai kaddamar kafin cikar wa’adinsa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya matsu kwana shida su cika saboda ba zai iya jure matsin lamba da yake fama da shi ba.

Buhari ya fadi haka ne a yayin taron cin abinci don karrama shi a ranar Talata 23 ga watan Mayu a Abuja wanda jami’an sojin kasar suka shirya.

Buhari a Yayin Taron
Shugaba Buhari a Yayin Taron Karramawa da Jami'an Soji. Hoto: Ripples
Asali: Facebook

Tribune ta tattaro cewa Buhari wanda ya zo latti wurin taron ya bayyana rashin zuwan nashi da wuri akan matsin lamba da yake samu yayin barin mulki.

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Kalamai Masu Ratsa Zuciya A Taron Bankwana

Ya kara da cewa a kwanakin nan yana fama da matsin lamba da kuma jerin tarurruka da kuma abubuwan da yake son kammalawa kafin barin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yawan ayyukan da suka yi wa Buhari yawa

Shugaba Buhari wanda ya jagoranci taron majalisar zartaswa, ya kuma kaddamar da ayyuka da dama da suka hada da kaddamar da ofishin jami’an yaki da fasa kwabri na kwastam kafin wannan taro inda ya nemi afuwa da su masa uzuri.

A cewarsa:

“Kuyi hakuri, bari na sauka akan hanya, ina neman afuwa saboda rashin zuwa da wuri, gaskiya ina samun matsin lamba sosai a kwanan nan, da kyar nake iya kammala jerin abubuwan da nake son yi, na matsu kwanaki shidan nan kare."

Buhari ya godewa jami'an tsaro

Buhari ya godewa jami’an tsaro saboda sadaukarwarsu ga tsaron kasa, ya bukace su da sauran jami’an tsaro da kada su gaji wurin tabbatar da tsaro a fadin kasar, cewar Ripples.

Kara karanta wannan

Gyaran Hali: Kotu Ta Umarci a Zane Wani Matashi Barawon Kaji Da Ransu Bulali 8 a Kaduna

Ya kara da cewa:

“Zan yi amfani da wannan dama don godewa jami’an sojin kasar nan akan jajircewarku da aiki tukuru da kuma goyon baya don samar da tsaro a kasar nan, ina sane da dukkan sadaukarwarku da jajircewa wurin dakile rashin tsaro musamman a lokacin zabe.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron akwai shugaban kamfanin mai na kasa, Mele Kyari da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, da shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote da ‘yan majalisun tarayya da kuma sauran manya-manyan baki.

Saura Kwanaki 6: Hanan Tayi Magana a Kan Mulkin Buhari

A wani labarin, daya daga cikin 'ya'yan shugaba Buhari, Hanan ta yabawa mahaifin nata kan yadda ya yi mulki.

Hanan ya bayyana haka ne a shafinta na instagram inda ta jinjinawa mahaifin nata akan ayyukan da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.