Mutane Hudu Sun Faɗa Komar ‘Yan Sanda a Ogun Bisa Laifin Halaka Makiyayi
- 'Yan sandan jihar Ogun sun kama wasu mutane 4 da suka halaka wani makiyayi da yake kiwon dabbobi kusa da ƙauyensu
- Ɗan uwan mamacin, wanda abin ya faru a gabansa ne ya kai ƙorafi wurin jami'an tsaro bayan faruwar lamarin
- 'Yan sandan sun sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da laifi a cikin mutanen da ake tuhuma
Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da kama wasu mutane huɗu da ake zargi da kashe wani makiyayi da aka yi gunduwa-gunduwa da gawarsa a ƙauyen Ijagunre da ke ƙaramar hukumar Imeko-Afon a jihar.
A makon da ya gabata ne Punch ta ruwaito cewa, rundunar Amotekun a jihar ta cafke biyu daga cikin waɗanda ake zargin gami da miƙa su hannun ‘yan sanda.
An kamo biyu daga cikinsu daga Oyo
An kuma bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta damƙe wasu mutanen biyu, daga bisani kuma aka miƙa su ga rundunar ‘yan sandan jihar Ogun domin gurfanar da su gaban ƙuliya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, a ranar Litinin din da ta gabata, ya tabbatar da kama mutane huɗun da ake zargi.
An bada sunayensu kamar haka: Akinyele Adebayo, Gbalo Idosu, Abiala Segun da Kareem Lana, waɗanda ake tuhuma bisa zargin kashe makiyayi Umaru Aliyu tare da sassara naman jikinsa.
Yadda lamarin ya faru
Oyeyemi ya ce kama su ya biyo bayan ƙorafi da wani Umaru Jakake ya gabatar, wanda ya bayyana cewa hakan ya faru ne yayin da shi da ɗan uwansa marigayin suka je kiwo a ƙauyen Ijagunre.
Ya ce wani manomi ne ya biyo su sai ya gargaɗe su cewa kada su zo da shanunsu kusa da gonarsa.
Jakake ya ƙara da cewa bayan sun kora shanun nasu ne, sai manomin daga baya ya kira wasu mutane su biyu sai suka bi su da gudu zuwa cikin daji.
Dakyar nasha a hannun manoma
Jakake ya ce shi ya yi nasarar tserewa, amma ɗan uwansa bai samu hakan ba, tun lokacin ba a ma ƙara jin ɗuriyarsa ba.
Jami'in ya ce binciken da sashen binciken kisan kai na rundunar ‘yan sandan da SP Kehinde Beyioku ya jagoranta, ya kai ga cafke waɗanda ake zargin a yayin da har yanzu ake neman manomin.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa manoman sun harbi Umaru Aliyu da bindiga ne, sannan suka yanke kansa domin yin tsafi.
Ya kara da cewa:
"yan sandan sun gano kan mamacin da sauran sassan jikinsa."
Oyeyemi ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olanrewaju Oladimeji, wanda ya yabawa tawagar da suka yi binciken, ya bayar da umarnin a nemo wancan da ya gudu.
Ya ƙara da cewa kwamishnan ya kuma bada umarnin gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Kada ku kai harin ramuwar gayya, CAN ta faɗawa kiristoci a Filato
A wani labari na daban kuma, ƙungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN, ta yi kira ga kiristocin a jihar Filato da kada su yi ramuwar gayya a hare-haren da ake kai musu a jihar.
Can ta ce an kashe sama da mutane 130, gami da ƙona gidaje sama da 1,000 a hare-haren.
Asali: Legit.ng