Jami’ar Ambrose Alli Ta Sallami Ma’aikata 13, Ta Ragewa Wasu Matsayi Saboda Rashawa Da Rashin Da’a

Jami’ar Ambrose Alli Ta Sallami Ma’aikata 13, Ta Ragewa Wasu Matsayi Saboda Rashawa Da Rashin Da’a

  • Kwamitin kula da da'ar ma'aikata na jami'ar Ambrose Alli (AAU) da ke Ekpoma ya sallami ma'aikata 13 saboda rashin da'a
  • Bayan haka, an ragewa wasu matsayi saboda aikata laifuka kamar yadda mukaddashin shugaban makarantar, Farfesa Asomwan Adagbonyi ya tabbatar
  • Adagbonyi ya bayyana cewa an kammala bincike kan batutuwa 132 kuma an zartar da hukunci a kansu yayin da wasu batutuwa 77 ke kasa

Edo - Gwamnatin jihar Edo karkashin jagorancin Gwamna Godwin Obaseki ta sallami lakcarori 13 na jami'ar Ambrose Alli (AAU) da ke Ekpoma.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an sallami lakcarorin ne kan zarginsu da aikata laifuka daban-daban da suka hada da karyar shekaru, zamba, rashin da'a, rashawa, lalata da sauransu.

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo
Jami’ar Ambrose Alli Ta Sallami Ma’aikata 13, Ta Ragewa Wasu Matsayi Saboda Rashawa Da Rashin Da’a Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Gaskiyar dalilin da yasa aka sallami malaman jami'ar AAU

Baya ga haka, an ragewa wasu adadi na ma’aikata matsayi kan aikata wasu laifuka, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Zababben ‘Dan Majalisa Zai Kinkimo Aiki, Yana So a Binciki Buhari Bayan Ya Sauka

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban jami’ar, Farfesa Asomwan Sunny Adagbonyin, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu, yayin da yake gabatar da rahoton kwamitin kula da da’a ta jami’ar ga mambobin tawaga ta musamman na jami’ar AAU.

A cewar Adagbonyin, an sallami ma’aikatan ne saboda shawarwarin da kwamitin kula da da’a na jami’ar ya bayar bayan ya same su da aikata laifukan da ake tuhumarsu a kai.

Shugaban makarantar ya kuma bayyana cewa an dakatar da wani mai shirin zama Farfesa da wani lakcara kan karbar wasu kudade ba bisa ka’ida ba daga wajen dalibai yayin da aka sallami wani lakcara wanda aka samu da lalata, rahoton THISDAY.

Gwamna Obaseki ya rushe Kwamishinoni Da Hadimansa

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya rushe majalisar zartarwarsa gabannin mika mulki ga sabuwar gwamnati.

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

An tattaro cewa Obaseki ya dauki matakin rushe majalisar ne a ranar Laraba, 3 ga watan Mayun 2023.

Majalisar zartarwar ta kunshi kwamishinoni, masu bayar da shawara na musamman da manyan hadiman gwamna.

Gwamna Obaseki ya bayyana cewa rushe su da ya yi daga kan muƙaman su, za ta fara aiki ne nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng