Zababben ‘Dan Majalisa Zai Kinkimo Aiki, Yana So a Binciki Buhari Bayan Ya Sauka

Zababben ‘Dan Majalisa Zai Kinkimo Aiki, Yana So a Binciki Buhari Bayan Ya Sauka

  • Philip Agbese yana so Gwamnatin da za ta karbi mulki ta binciki nade-naden Muhammadu Buhari
  • Laifin shugaban kasa mai barin-gado a wajen zababben ‘dan majalisar shi ne nadin wasu mukamai
  • Cif Agbese ya ce bada mukamai da ake yi a kurarren lokaci ya nuna akwai alamar tambaya a gwamnati

Abuja - Zababben ‘dan majalisar wakilan tarayya, Philip Agbese, ya yi kaca-kaca da Muhammadu Buhari a dalilin nade-naden mukamai da ya ke yi.

Leadership ta ce Cif Philip Agbese bai gamsu da yadda ake nada jami’an gwamnatin tarayya a daidai lokacin da wa’adin gwamnati ya zo karshe ba.

Da yake jawabi kwanaki a garin Abuja, Jigon na jam’iyyar APC ya yi kira ga Asiwaju Bola Ahmed ya binciki mukaman karshe da aka bada a gwamnati.

Buhari
Muhammadu Buhari, mai dakinsa, SGF da Gambari Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Ganin an ba mutane akalla 10 mukamai a makon da ya gabata, Agbese ya fito ya na cewa kyau a bar gwamnati mai jiran-gado ta raba mukaman nan.

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar ‘dan siyasar, irin wadannan mukamai da ake badawa a karshen wa’adin gwamnati mai-ci zai lalata aiki, ya kuma jawo satar dukiyar al’umma.

An hada Tinubu da aiki

An rahoto Agbese ya na mai zargin Muhammadu Buhari da jefa magajinsa cikin matsala domin ana gaggawar bada mukamai ba tare da bin doka ba.

Zababben ‘dan majalisar na mazabun Ado, Okpokwu da Ogbadibo a jihar Benuwai ya bada misali da nadin sabuwar Akanta Janar ta Najeriya da aka yi.

Baya ga nadin sabuwar AGF, Agbese ya ce Mai girma Buhari ya yi nadin mukamai fiye da 20 daga lokacin da Bola Tinubu ya lashe zaben Najeriya.

"Tabbatar da Toyin Madein a kujera mai muhimmanci irin Akanta Janar ta kasa daf da gwamnatin nan za ta sauka ya jawo alamomin tambaya.
Gaggawar me ake yi? Su na kokarin boye wani abin ne?

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai Ya Zargi Tsoffin Gwamnonin Jihar da Satar Kudaden Al’umma Don Gina Gidaje a Dubai

-Philip Agbese

An saba doka a NEDC

This Day ta ce ‘dan siyasar ya nuna sashe na 171 na kundin tsarin mulki ya ba shugaban kasa damar nada mukamai, amma ba a irin wannan yanayi ba.

Ko an yafe batun nadin Maiden, sabon ‘dan majalisar zai so a duba lamarin shugabannin NEDC da suka soma aiki ba tare da majalisa ta tantance su ba.

Za a kaddamar da ayyuka

Labari ya zo cewa Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabuwar Hedikwatar kwastam da aka gina, wannan aiki ya ci kusan Naira Biliyan 20 a Najeriya.

Haka zalika an gama gadar Neja, gadar Loko-Oweto da gadar Ikom Bridge da titin Kaduna-Kano da wasu Sakatariyoyi a garuruwan Gusau, Yenagoa da Awka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng