NAHCON Ta Sauya Magana Kan Batun Ƙarin Kuɗin Kujerar Hajjin Bana 2023

NAHCON Ta Sauya Magana Kan Batun Ƙarin Kuɗin Kujerar Hajjin Bana 2023

  • Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta yi amai ta lashe kan karin kuɗin kujerar Hajjin bana 2023.
  • A wata sanarwa yau Litinin, hukumar tace kowane maniyyaci zai ƙara dala $100 bayan gwamnati fa kawo tallafi
  • An samu karin $250 sakamakon rikicin Sudan, da farko hukumar ta ce ba zai shafi maniyyata ba amma komai ya canja a yanzu

Abuja - Hukumar kula aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta janye alƙawarin da ta ɗauka cewa maniyyata ba zasu biya ko sisi daga cikin ƙarin dala $250 da aka samu kan kowace kujerar Hajji ba.

Daily Trust ta tattaro cewa kamfanonin jiragen sama masu aikin jigilar maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki sun nemi ƙarin dala $250 kan kowace kujera saboda rikicin da ya ɓarke a ƙasar Sudan.

NAHCON
NAHCON Ta Sauya Magana Kan Batun Ƙarin Kuɗin Kujerar Hajjin Bana 2023 Hoto: NAHCON
Asali: UGC

A cewarsu, wannan faɗa da ya kaure a Sudan, zai haddasa yin shatale-shatale a hanyar zuwa ƙasar Saudiyya, sakamakon haka suka nemi ƙarin waɗanda nan kuɗi.

Kara karanta wannan

"Ta Ciri Tuta": Kyakkyawar Bahaushiya 'Yar Najeriya Ta Zama Soja a Amurka, Bidiyonta Ya Yadu Sosai

Amma da yake jawabi a wurin taron da hukumar ta shirya wa ma'aikatanta na ƙasa, jihohi da kuma masu zaman kansu, shugaban NAHCON, Zikrullah Hassan, ya tabbatar da cewa ƙarin ba zai shafi maniyyata ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NAHCON ta yi amai ta lashe

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na hukumar NAHCON, Moisa Ubandawaki, ya fitar ranar Litinin, ya ce hukumar ta yanke kowane maniyyaci zai biya ƙaso 40% na ƙarin da aka samu.

A cewarsa, ya kama kowane maniyyaci zai biya ƙarin dala $100 bayan gwamnatin tarayya ta ɗauki wasu nauye-nauyen jiragen saman da zasu yi aikin jigilar a bana.

A rajoton Punch, Sanarwan ta ce:

"Wannan matakin zai ƙara sauƙaka kuɗin kujerar Hajji da ake buƙatar kowane mai niyya ya biya. Tun da farko gwamnatin ta ɗauke wa maniyyata kaso 65% na wasu tsarabe-tsaraben harkokin sufurin jiragen sama."

Kara karanta wannan

Matatar Dangote: Ina Farin Ciki Don Zan Bar Najeriya Hannun Jajirtattu, Buhari

Daraktan ya ƙara da cewa idan ma'aikatar sufurin jiragen sama ta Sudan ta buɗe hanya komai ya koma daidai gabanin fara jigila, za'a maida wa kowane Alhaji kuɗinsa.

NAHCON Ta Sanar da Kuɗin Kujerar Sauke Farali, Ta Raba Su Zuwa Kaso 8

A wani Rahoton kuma Hukumar kula ta harkokin Hajji ta bayyana jerin kuɗin kujerar Hajjin bana 2023, ya kasu zuwa gids 8.

An samu karin kuɗin Hajji ne sakamakon tashin farashin dala a Najeriya, shugaban NAHCON ya yi magana mai muhimmanci

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262