Atiku 100; Peter Obi 50: Adadin Shaidun da Za Su Ba da Shaida a Kotun Raba Gardanar Zabe Game Murdiyar Tinubu

Atiku 100; Peter Obi 50: Adadin Shaidun da Za Su Ba da Shaida a Kotun Raba Gardanar Zabe Game Murdiyar Tinubu

  • Dukkan jam’iyyun siyasar da suka maka APC, INEC da Tinubu a kotu kan zaben 25 ga watan Faburairu za su gabatar da shaidu
  • Peter Obi na jam’iyyar Labour zai kawo shaidu 50 gaban kotu, ya kuma bukaci a bashi makwanni bakwai
  • Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya ce zai kawo shaidu 100 domin kalubalantar nasarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC
  • Hakazalika, Tinubu, APC da INEC sun fadi adadin shaidun da za su gabatar a gaban kotun nan ba da jimawa ba

FCT, Abujadukkan jam’iyyun da suka shigar da kara a kotun raba gardamar zabe sun nemi a basu damar gabatar da shaidunsu na cewa Bola Tinubu, zababben shugaban kasan Najeriya bai ci zabe ba.

Sun bayyana hakan ne a zaman da aka yi a ranar Asabar 20 ga watan Mayu a kotun, kamar yadda Arise News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

To Fah: Kwankwaso, Wike da Wasu Yan Adawa 4 da Ka Iya Shiga a Dama Dasu a Mulkin Tinubu

Adadin shaidun da za a gabatar a kotun zabe
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasan Najeriya | Hoto: Asiwaju Bola Ahmad Tinubu
Asali: Facebook

Peter Obi zai kawo shaidu 50 a gaban kotu

Peter Obi na jam’iyyar Labour ya bukaci a bashi damar gabatar da shaidunsa a gaban kotun don tabbatarwa alkalai cewa, tabbas an yi murdiya a zaben 25 ga watan Faburairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan na fitowa ne ta bakin lauyansa, Awa Kalu (SAN), inda yace yana bukatar a bashi makwanni bakwai don yin hakan.

Ya kara da cewa, za su bukaci makwanni bakwai ne saboda kalubalen da suke fuskanta na tattara hujjoji daga na’urar zabe ta BVAS.

Tinubu zai kawo shaidu 21 game da karar Obi

A bangare guda, Bola Ahmad Tinubu zai ba da shaidu 21 game da karar da Peter Obi ya shigar a kansa a gaban kotun.

Hakan ya fito ne daga bakin lauyansa, Rowland Otaru (SAN), inda ya nemi a basu kwanaki tara don yin hakan.

Kara karanta wannan

Murnar APC ta koma ciki: Atiku ya kada hanjin Tinubu, zai kawo shaidu 100 gaban kotu

APC za ta gabatar da shaidu bakwai game da karar Obi

A bangaren APC, ta ce za ta gabatar da kwararan shaidu da ke nuna nasararta a zaben shugaban kasa a karar da Obi ya shigar.

Lauyan APC, Niyi Akintola ne ya bayyana hakan, inda ya nemi a ba APC kwanaki bakwai kacal don tabbatarwa da kotu Tinubu ne ya lashe zabe daga bakin shaidu.

INEC za ta ba da shaidu biyu game da karar Obi

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ce shaidu biyu kadai za ta gabatat game da karar da Obi ya shigar kan cewa an yi murdiya a zaben shugaban kasa.

Lauyan INEC, Abubakar Mahmood (SAN) ne ya fadi hakan, inda yace kwanaki uku kadai sun isa don kawo wadannan hujjoji da shaidu.

Atiku zai kawo shaidu 100 don kalubalantar nasarar Tinubu

A bayanan da lauyan Atiku, Chris Uche ya gabatar, ya ce akwai shaidu 100 da zai gabatar don nunawa duniya Tinubu bai lashe zabe ba.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, An Fallasa Babban Dalilin da Ya Sa Kwankwaso Bai Kalubalanci Nasarar Tinubu Ba a Kotu

A cewarsa, yana bukatar makwanni uku ne kacal domin gabatar da shaidun da ke nuna INEC bata yi gaskiya a zaben na bana ab.

Tinubu zai kawo shaidu 39 don musanta ikrarin Atiku

A bangaren shari’arsa da Atiku, Tinubu ya ce yana da shaidu 39 da zai gabatarwa kotun raba gardamar zabe.

Lauyansa, Wole Olanipekun ne ya fadi hakan, inda yace kwanaki tara kadai sun wadatar don kawo shaidun da ake bukata.

APC za ta kawo shaidu 25 don dakile ikrarin Atiku

Lauyan APC, Solomon Umoh (SAN) ya ce zai kawo shaidu 25 a madadin jam’iyyar don tabbatar da cewa Tinubu ya lashe zabe.

Wannan kenan ta bangaren APC baya ga adadin shaidun da tace za ta kawo game da karar Obi a baya.

INEC za ta kawo shaidu biyar game da karar Atiku

A bangaren INEC, ta ce tana da shaidu biyar da za ta gabatar a gaban kotu don tabbatar da bata yi rashin gaskiya ga sakamakon zaben ba.

Kara karanta wannan

"Tinubu Ba Zai Wuce Wata 6 Zuwa 7 a Kan Kujerar Shugaban Ƙasa Ba," Babban Jigo Ya Faɗi Abinda Zai Faru

Bayan haka, kotun ta dage ci gaba da sauraran karar har zuwa ranar Litinin, 22 ga watan Mayu idan Allah ya kaimu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.