Bayan Shafe Shekaru 7 Ana Abu Daya, Dalibin Likitanci Ya Yi Jarrabawar Karshe, Ya Cancare da Rawa

Bayan Shafe Shekaru 7 Ana Abu Daya, Dalibin Likitanci Ya Yi Jarrabawar Karshe, Ya Cancare da Rawa

  • Wani dalibin likitanci a Najeriya ya cancare da rawa bayan da ya rubuta jarrabawar karshe a karatunsa na digiri
  • A bidiyon da @lawrence.hezekiah_ ya yada a TikTok ya nuna yadda dalibin ya yiwa rigarsa rubuce-rubucen kammala karatu
  • Sauran dalibai sun taru, inda suka tsaya kallonsa a lokacin da yake taka rawa don murnar cimma nasarar rayuwa

Bayan rubuta takardar karshe a karatun jami’a, dalibin likitanci ya cancare da rawa a bainar jama’a don nuna farin cikinsa.

Dan TikTok, @lawrence.hezekiah_ ne ya yada bidiyon da ke nuna yadda dalibin ke murna a tsakiyar makaranta.

A bidiyon, an ga sauran dalibai da ke cikin farin ciki sun taru a lokacin da dalibin na likitanci kuma likitan gobe ke taka rawa.

Dalibin likitanci ya cancare da rawa
Lokacin da dalibin ke tika rawa a bainar jama'a | Hoto: @lawrence.hezekiah_.
Asali: TikTok

Ya taka rawa sosai, har ta kai jama’a suka tsaya suna kallonsa a lokacin da yake ta dagewa yana tikar rawa kamar ba gobe.

Kara karanta wannan

Yadda Muka Rasa ’Yan Uwanmu a Harin ’Yan Bindiga, Mutane Sun Koka a Jihar Plateau

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yana sanye da farar riga da farin wando da kuma bakaken safa, wanda ke nuna musamman ya shirya wannan rawa tsaf.

Sauran daliban da suka kammala karatu tare su ma suna cikin farin ciki, amma basu tiki rawa kamar yadda ya yi ba.

Tsabar yadda yake rawa, sauran daliban sun tsaya ne kawai suna yi masa ihun jin dadi da kuma annashuwa.

Bidiyon, wanda ya yadu sosai, ana kyautata zaton an dauke shi ne a cikin jami’ar jihar Abia da ke Kudancin Najeriya.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

@_valentinadgaf:

"Tika rawarka yaro! Ka cancanci hakan.”

@mimi love:

"Ina taya ka murna dan uwa. Na kagu na ga nawa ranar.”

@anichinazaoly:

"Ina taya ka murna dan uwa. Rawarka abin burgewa ne.”

@itzvictoria:

"Wannan ya yi kyau yaro...ina taya ka murna.”

@ANN-JAEH:

"Ka dawo don Allah. Wannan makarantar ta rike min kai sosai. Ina taya ka murna masoyina.”

Kara karanta wannan

Rashin Aiki Ko Kwakwaf: ’Yar Najeriya Ta Bude Buhun Shinkafa, Ta Fara Kirge Don Sanin Kwaya Nawa Ne a Ciki

@tennehsamura34:

"Ina taya ku murna duka. Babu sauki amma Allah ya dafa muku.”

@keisa_peng:

"Ka cancanci wannan rawar. Babu sauki.”

Mata mai sana'ar shara da ke samun fiye da albashin likitoci

A wani labarin, wata mata ta ce tana samun kudin da ya fi na albashin likitocin Najeriya, inda tace sana'arta ita ce yin sharar titi.

Jama'ar kafar sada zumunta sun yi mamaki, sun ce za su ajiye ayyukansu domin yin shara idan suka samu dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.