Rashin Aiki Ko Kwakwaf: ’Yar Najeriya Ta Bude Buhun Shinkafa, Ta Fara Kirge Don Sanin Kwaya Nawa Ne a Ciki

Rashin Aiki Ko Kwakwaf: ’Yar Najeriya Ta Bude Buhun Shinkafa, Ta Fara Kirge Don Sanin Kwaya Nawa Ne a Ciki

  • Wata budurwa ‘yar Najeriya ta dukufa a kokarinta na ganin ta kirga buhun shinkafa don kafa tarihi a duniya
  • Wani matashi mai suna @prize303 ne ya wallafa faifan bidiyon a kafar sada zumunta inda aka gano ta na ta kirgen
  • Faifan bidiyon ya jawo martanin mutane da dama inda wasu ke cewa meye yasa ba za ta dafa shinkafar ta cinye ba

A kokarinta na kafa tarihi a duniya, ‘yar Najeriya ta fara kirga buhun shinkafa don tabbatar da yawansu a ciki.

Wani mai suna @prize303 ya wallafa faifan bidiyo inda ya nuna yadda budurwar cikin natsuwa ke kirga shinkafar dake cikin buhun da kuma lissafa yawan abin da ta samu.

budurwa/bidyo
Yar Najeriya Ta Bude Buhun Shinkafa, Ta Fara Kirge Don Sanin Kwaya Nawa Ne a Ciki. Hoto: @prize303
Asali: TikTok

Budurwar ta sha alwashin cewa sai ta kirga dukkan shinkafar dake cikin buhun ba tare da ta gajiya ba.

Kara karanta wannan

Ina Matukar Son Matata: Fasto Ya Roki Alkali Kada Ya Datse Igiyar Aurensa

Faifan Bidiyon da aka yada, ya jawo martani daga masu ta’ammali da kafar sada zumunta, sai dai abin da ba a tabbatar ba shi ne girman buhun shinkafar amma a yanzu haka ta kirga tsabar da ta kai 13,000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin kirgen, ta na rike da takarda da take rubuta duk abinda ta kirga don kada ta manta, wasu daga cikin mutanen da suka maida martani sun mata shaguben cewa ta dafa shinkafar ta cinye mana.

Ga faifan bidiyon a kasa:

Martanin jama’a akan bidiyon

@user8690973620191:

“Wannan shi ne addu’a na kullum, kada Allah yabar makiya na ba aiki, amen.”

@kiwi:

“Kina son ki kafa tarihin Guiness Record da wannan kirge? Da wannan shiriritan? Ina miki fatan nasara.”

@christineuwanyana:

“Ba kya jin yunwa ne da ba za ki cinye shinkafan ba.”

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

@Mytrust:

“Lallai kina da isasshen lokaci.”

@Ose, Unique Sosa:

“Ina miki fatan nasara.”

@Ruff1z:

“Wannan za ta iya nasara da kuma kafa tarihi na Coca-Cola.”

@user7475126631361:

“Ina so ki kirga min gashin kai na.” “Ke kika sani.”

Budurwa ta Fashe da Kuka Saboda Rashin Ciniki a Shagonta

A wani labarin, an gano wata budurwa ta fashe da kuka a shagonta saboda rashin ciniki har na tsawon makwanni uku.

Budurwar ta ce duk da rage farashin kayan shagon ta amma cikin makwanni babu wanda yazo ya sayi ko da abin kwandala a shagon nata na kayan kawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel