Innalillahi: Mutane Da Dama Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota Kan Titin Hanyar Lokoja-Abuja

Innalillahi: Mutane Da Dama Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota Kan Titin Hanyar Lokoja-Abuja

  • Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wata motar tanka ɗauke man fetur akan titin hanyar Lokoja-Abuja
  • Hatsarin ya auku ne lokacin da motar tankar ta ƙwacewa direbanta inda ta haɗe da wata mota mai tahowa daga ɗayan hannun titin
  • Ana fargabar cewa mutane da dama sun ƙone ƙurmus a sakamakon gobarar da ta tashi bayan motocin sun yi taho mu gama

Jihar Kogi - Mutane da dama sun ƙone ƙurmus a wani mummunan hatsarin mota kan titin hanyar Lokoja-Abuja a jihar Kogi.

Wani ganau ba jiyau ba ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, hatsarin ya auku ne lokacin da wata tanka maƙare da man fetur ta ƙwace ta yi taho mu gama da sauran motocin da ke tahowa a a ɗaya ɓangaren titin.

Mutane da dama sun kone kurmus a wani mummunan hatsarin mota a jihar Kogi
'Yan kwana-kwana na kokarin kashe wuta (Ba inda hatsarin ya auku ba) Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Wani mai suna Yusuf daga Kotonkarfe, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun isa wajen domin ƙoƙarin kashe wutar da ta ke da ci ba ƙaƙƙautawa.

Kara karanta wannan

“Na Fi Karfin Mace Daya”: Wani Mutum Dan Shekara 63 Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Ce Zai Kara Aure

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Motar tankar yanzu haka tana ci da wuta da sauran wasu motocin da hatsarin ya ritsa da su. Na ga motocin haya guda biyu da wasu motoci na ci da wuta. Jami'an tsaro ciki har da jami'an hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC), na iyakar bakin ƙoƙarin su wajen kashe wutar da ceto fasinjojin da suka maƙale a cikinta."

A cewarsa, hatsarin ya auku ne a gaban sakatariyar ƙaramar hukumar Kotonkarfe

Ana ci gaba da ƙoƙarin ceto fasinjojin

Kwamandan hukumar FRSC ta jihar, Stephen Dawlung, ya tabbatar da cewa an tura jami'an hukumarsa zuwa wajen da hatsarin ya auku, cewar rahoton Aminiya.

Kwamandan ya kuma bayyana cewa har yanzu motar tankar man fetur ɗin na ci gaba da ci da wuta.

A kalamansa:

"Jami'an mu suna wajen yanzu haka. Babu wani cikakken bayani har yanzu. Motar tankar na ci da wuta yanzu haka, wanda hakan ya janyo matsalar wucewar ababen hawa akan titin. Zan ba ku cikakkun bayanai da zarar mun kammala."

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Wani Dattijo Gidan Yari Saboda Sarrafa Kwandala Da Ficika Zuwa Kayan Ado A Kano

Legit Hausa ta samo jin ta bakin ƙanin direban motar tankar mai suna Hassan Lawal, wanda ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko ɗaya ba a mummunan hatsarin motar da ya auku.

Hassan ya bayyana cewa motar ƴaƴan na sa tana cikin tafiyar ta ne kawai wacce ɗayar motar ta ta tsallako daga hannunta ta zo ta buga musu, inda wuta ta tashi nan da nan.

Ya bayyana cewa motar tankar yayan na sa ba za ta sake moruwa ba domin ta ƙone ƙurmus.

Ayarin Motocin Gwamnan Ebonyi Sun Gamu da Hatsari, Mutum Uku Sun Mutu

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa ayarin motocin gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, sun gamu da wani mummunan hatsarin mota.

Hatsarin motar wanda ya ritsa da kwamban motocin gwamnan, ya yi sanadiyyar ajalin mutum uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng