Hotunan Yadda Shettima, Ganduje, Da Wasu Manyan Jiga-Jigan APC 3 Lokacin da Suka Maranci Tinubu

Hotunan Yadda Shettima, Ganduje, Da Wasu Manyan Jiga-Jigan APC 3 Lokacin da Suka Maranci Tinubu

  • Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan shafe kwanaki takwas a kasar ketare
  • Tinubu ya samu tarba daga jiga-jigan jam’iyyar APC da suka hada da mataimakinsa Kashim Shettima da gwamna Ganduje
  • Sauran sun hada da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa Idris Wase

Abuja Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya a ranar Asabar 20 ga watan Mayu inda ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja babban birnin kasar.

A wasu hotuna da Legit.ng Hausa ta samu daga ofishin Tinubu ta hannun Tunde Rahman, Tinubu ya samu gagarumar tarba daga jiga-jigan na jam’iyyar APC.

Dawowar Tinubu Najeriya
Ganawar Tinubu da su Ganduje bayan dawowa daga Najeriya | Hoto: Tunde Rahman
Asali: Twitter

Jerin wadanda suka tarbi zababben shugaban kasan a Abuja

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Muhimman Bayanai Sun Fito Yayin da Bola Tinubu Ke Shirin Dawowa Najeriya

A cewar Tunde Rahman:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya samu tarba daga shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma mataimakin shugaban majalisar wakilai Idris Wase a Abuja a ranar Asabar 20 ga watan Mayu.”

Daga cikin hotunan, Tinubu ya samu tarba daga zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da Godswill Akpabio wanda jam’iyyar ta zaba a matsayin wanda zai gaji kujerar shugabancin majalisar dattawa.

Sirrin Ganduje ya fito, duk da haka ya gana da Tinubu

Gwamna Ganduje na Kano shima ya halarci tarbar zababben shugaban bayan da wani faifan muryan da aka nada na gwamnan ya yadu a lokacin da yake sukar ganawar Tinubu da Kwankwaso.

Mun kawo muku yadda Tinubu ya shafe sa’o’i hudu yana ganawa da Kwankwaso a birnin Paris na kasar Faransa, inda ake tunanin sun tattauna ne akan yadda za su yi aiki tare a sabuwar gwamnatin da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Shugaba Buhari Ya Sanar da Muhimmin Abu 1 da Zai Wa Tinubu da Shettima Kafin Ya Sauka

Ganduje ya ce Tinubu ya yaudare shi

A faifan da aka nada a boye, Ganduje ya bayyana yaudararsa da Tinubu ya yi dalilin ganawarsa da Kwankwaso a Paris.

Sai dai, a lokacin da yake babatun, Ibrahim Masari wanda Tinubu ya taba zaba a matsayin mataimaki ya shawarci Ganduje da ya hakura su tattauna da Tinubu a hankalce.

A bangare guda, hasashe na nuna cewa, akwai yiwuwar Tinubu ya dauko su Kwankwaso domin damawa dasu a mulkinsa da zai fara ranar 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.