Shari’ar Zabe: Atiku Zai Kira Shaidu 100 Kan Karar da Ya Shigar Ta Kalubalantar Tinubu
- Yayin da ake ci gaba da shirin rantsar da Bola Ahmad Tinubu a kujerar shugabancin kasa, ana ci gaba da shari’a a kotun raba gardamar zabe
- Atiku ya kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu, inda yace bai amince Tinubu ya maka shi da kasa ba
- Ya zuwa yanzu, an yi zama sama da biyu, yanzu dai Atiku ya ce zai kawo shaidu 100 don gaban kotun nan ba da jimawa ba
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya nemi a bashi damar gabatar da shaidu 100 a gaban kotun raba gardamar zabe a karar da ya shigar na kalubalantar nasarar Tinubu.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana bukatar tsaida shaidu 22, inda Tinubu zai kawo shaidu 39 sai kuma APC mai son kawo 25 don kare kai.
Batun na Atiku na fitowa ne daga bayanan da aka caccaka tsinke a kansu a cikin zaman da aka yi na shari’ar kalubalantar Tinubu a nasararsa ta zaben 25 ga watan Faburairu, rahoton Daily Trust.
Bangarorin hudu sun kuma nemi a kara ba su lokaci domin samun damar zantawa da kwararan shaidun da suke dashi cikin mintuna 20 zuwa 30, inda tuni aka kira wasu daga cikin shaidun don rantsewa a gaban kotu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Lauyan Atiku ya fadi adadin lokacin da yake bukata
Lauyan Atiku, babban lauya Chris Uche (SAN) ya kuma bayyana cewa, doka ta ba su ikon gabatar da hujjoji da shaidunsu a cikin makwanni bakwai, amma suna bukatar a basu makwanni uku ne kacal don yin hakan.
A cewarsa:
“Batutuwan ba su da wata sarkakiya kuma galibi sun shafi tsarin mulki; don haka ba za su bulaci wani dogon lokaci mai yawa ba don tantancewa. Misali, batun FCT.”
A bangare guda, kotun ta dage ci gaba da zamanta har zuwa ranar Litinin, 22 ga watan Mayi don ci gaba da sauraran jawabai, TheCable ta tattaro.
Ba Atiku kadai ne ya shigar da kara ba
A ranar ta Litinin, kotun za ta saurari kararrakin da sauran jam’iyyun siyasa uku suka shigar game da kalubalantar Bola Ahmad Tinubu.
Idan baku manta ba, bayan nasarar Tinubu, jam’iyyu da ‘yan takararsu da yawa sun nuna adawa da nasarar.
Peter Obi na jam’iyyar Labour, wanda ya zo na uku a zaben na daga cikin wadanda suka kalubalanci sakamakon zaben.
Asali: Legit.ng