'Yan Sanda Sun Gabatar Da Takardun Da Ke Kunshe Da Bayanan Tuhumar Alhassan Doguwa
- Ƴan sanda a jihar Kano sun gabatar da takardun bayanan tuhumar da ake yi wa Alhassan Ado Doguwa a gaban ma'aikatar shari'ar jihar
- Kwamishinan shari'a na jihar ya tabbatar da karɓar takardun bayanan daga wajen kwamishinan ƴan sandan jihar
- Sai dai, ma'aikatar shari'ar ta sake mayar da takardun bayanan ga ƴan sanda inda ta nemi su ƙaro mata hujjoji waɗanda za su sanya a gurfanar da Doguwa
Jihar Kano - Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan, ya tabbatar da cewa rundunar ƴan sandan jihar ta gabatar da rahoton ta ga ma'aikatar shari'a kan zargin kisan da ake yi wa, Alhassan Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai.
Daily Trust tace da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya ƙarbi takardar bayanan a ofishinsa ranar Juma'a 19 ga watan Mayun 2023, Antoni Janar ɗin ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sanda jihar ya kawo takardar bayanan.
Ya ce kwamishinan ya kawo takardar da ke ɗauke da bayanan ne da misalin ƙarfe 12:45 na ranar Juma'a.
A kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina so na tabbatar wa da jama’a cewa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, za mu yi nazari kan takardar bayanan domin bayar da shawarar mu kan shari’ar."
Kwamishinan Shari’ar jihar ya sanar da cewa ma’aikatar ta sake mayar da rahoton ga ƴan sanda domin su ci gaba da bincike, inda ta nemi samun ƙarin bayani kan zarge-zargen da ake yi wa Doguwa waɗanda za su bayar da hurumin gurfanar da shi a gaban kotu, cewar rahoton Aminiya.
Daga cikin bayanan da ma’aikatar shari'ar ta buƙata har da hotunan gawarwakin waɗanda aka kashe, bayanan shaidu da bindigar da aka kwato da sauran abubuwan da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifukan, domin tabbatar da an aikata laifin kamar yadda ake tuhuma.
Tuhumar Kisa Ba Za Ta Hana Ni Neman Mukami Ba -Ado Doguwa
A wani rahoton na daban kuma, Alhassan Ado Doguwa ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada a majalisar wakilai, ya ce shi ba mai laifi ba ne har sai idan kotu ta tabbatar.
Ado ya ce zargin da ake masa ba zai hana shi neman takarar kujerar shugabancin majalisar wakilai ta 10 ba.
Asali: Legit.ng