"Ba Zamu Yi Sa'insa da Kai Ba," EFCC Ta Maida Martani Ga Gwamna Matawalle

"Ba Zamu Yi Sa'insa da Kai Ba," EFCC Ta Maida Martani Ga Gwamna Matawalle

  • Hukumar EFCC ta ce ba zata tsaya jayayya da gwamna Bello Matawalle ba, wanda take tuhuma da karkatar da makudan kudi
  • Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya maida martani kan zargin da gwamnan ya ɗora wa shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa
  • Alaka na ƙara tsami tsakanin gwamnan Zamfara da EFCC tun bayan fara tuhumarsa da kwashe kuɗin a asusun jiharsa

Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ce ba zata tsaya tana sa'insa da gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Bello Matawalle, ba.

Daily Trust ta rahoto cewa EFCC ta faɗi hake ne yayin martani kan zargin da Matawalle ya ɗora wa shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa.

EFCC.
"Ba Zamu Yi Sa'insa da Kai Ba," EFCC Ta Maida Martani Ga Gwamna Matawalle Hoto: EFCC
Asali: UGC

Matawalle, wanda ya shiga takun saƙa da EFCC a 'yan kwanakin nan, ya yi ikirarin cewa Bawa ya nemi cin hancin $2m a wurinsa amma ya hana shi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami'an Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa, Sun Aiko da Sako Mai Ta Da Hankali

A wata hira da sashin Hausa na BBC, Gwamnan Zamfara ya ce shugaban EFC ba mutumin arziki bane kuma yana da kwararan shaidu a kansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin martani kan wannan ikirari a wata sanarwa da kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar ranar Jumu'a, ya misalta Matawalle da mutumin da ruwa ke shirin cinyewa.

Ya ce EFCC ba zata tsaya tana ɓata lokacinta wajen jayayya da wanda ake tuhuma da wawure kuɗin talakawa ba kuma ya kalubalanci Matawalle, "Kar ya hakura, ta fasa kwan kowa ya ji."

Wani sashin sanarwan ya ce:

"An jawo hankalinmu kan wata hira da sashin Hausa na BBC suka yi da Muhammad Bello Matawalle, gwamnan Zamfara, inda ya ɗora zargin cin hanci kan shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa.”
"Kalaman Matawalle shure-shure ne da baya hana mutuwa kuma ya yi kama da mutumin da ke nutsewa a ruwa, ya kama karmami. Duk da ikirarin da ya yi, EFCC ba zata tsaya jayayya da wanda take tuhuma da wawure kuɗin jiharsa ba."

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: "Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin $2m Daga Wuri Na," Gwamnan APC Ya Fasa Ƙwai

"Idan kuma kalaman Matawalle gaskiya ne, bai kamata ya tsaya yana ɓaɓatu ba, ya nufi gaba inda zai gabatar da shaidun da zasu gamsar da zargin da yake gaskiya ne."

Wasu na kokarin guduwa bayan mika mulki - EFCC

Bugu da ƙari EFCC ta ƙara ankarar da ɗaukacin al'umma cewa wasu gurɓatattun 'yan siyasa da ake tuhuma da wawure kuɗin gwamnati na shirin guduwa daga ƙasar nan gabanin 29 ga watan Mayu.

A cewar EFCC, tana kokarin haɗa kai da takwarorinta na ƙasashen duniya domin daƙile wannan yunkuri da kuma tabbatar da doka ta yi aikinta.

Ganduje ya maida martani ga Abba Ƙabir Yusuf

A wani rahoton na daban, Ganduje ya tona yadda Kwankwaso ya fara sayar da gidajen gwamnatin jihar Kano a zamanin mulkinsa.

Da yake martani ga wasu kalaman Abba Gida-Gida, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce sayar da kadarorin gwamnatin Kano ba yau aka fara ba kua yanzun za'a dena ba.

Kara karanta wannan

Babba Dalilin Da Yasa Gwamnan APC Ya Yi Shiru Kan Zargin da Ake Masa Na Wawure N70bn

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262